Labarai
Zamfara: NSCDC ta tura jami’ai 365 domin tabbatar da tsaro a bikin Easter
Rundunar tsaro ta farin Kaya wato Civil defense reshen Jihar Zamfara ta ce ta tura jami’anta 365 domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro yayin bikin Easter na shekarar 2026.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar na jihar, ASCI Umar Mohammad, ya fitar, inda ya ce an tura jami’an ne domin aiki kafin, lokacin da kuma bayan bukukuwan Easter.
Sanarwar ta ce matakin na da nufin ƙarfafa tsaro a wuraren ibada da kuma kare rayuka da muhimman kayayyaki a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.
Kwamandan NSCDC na jihar, CC Sani Mustapha, ya umarci jami’an su kasance masu ladabi, ƙwarewa da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan.
Ya kuma jaddada cewa hukumar na ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma muhimman kayan more rayuwa a faɗin jihar.
Sani Mustapha ya yi kira ga jama’a musamman Kiristoci da su gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali, tare da fatan cewa lokacin zai ƙara haɗin kai da zaman lafiya a ƙasar.
Aminu Dalhatu/Gusau
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
