Labarai
Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Yi Kira Da A Karfafa Mata
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta bukaci hukumomin gwamnati, abokan hulda na ci gaba, sarakuna, malamai da kamfanoni masu zaman kansu su hada kai wajen samar da yanayin da zai bai wa mata da ’yan mata damar cimma burinsu.
A sakon da ta fitar domin bikin Ranar Mata ta Duniya ta 2026, Hajiya Huriyya ta ce taken bana “Give to Gain” na nuna muhimmancin zuba jari a kan mata ta hanyar ba su ilimi, horo da damar samun albarkatu.
Ta ce mata na taka muhimmiyar rawa wajen gina iyali, karfafa al’umma da kuma bunkasa tattalin arziki da zamantakewa.
Ta kuma tabbatar da cewa ofishinta zai ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke taimaka wa mata da ’yan mata musamman a bangarorin lafiya, ilimi, sana’o’i da walwalar jama’a.
Hajiya Huriyya ta kuma bukaci mata a Zamfara su ci gaba da jajircewa wajen ba da gudunmawa ga ci gaban jihar, tare da amfani da sauran kwanakin Ramadan wajen yi wa Zamfara da Najeriya addu’ar zaman lafiya da ci gaba.
Aminu Dalhatu/Gusau
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
