Connect with us

Labarai

Gwamna Lawal Ya Nada Darakta Janar Na Asusun Hanyoyin Zamfara

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗin Bashir Abdullahi Gusau a matsayin Darakta Janar na Asusun kula da Hanyoyin jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Abubakar Mohammad Nakwada, ya ce naɗin ya biyo bayan kafa dokar Asusun kula da Hanyoyin Zamfara.

Sanarwar da mai taimaka wa Sakataren gwamnatin jihar kan yaɗa labarai, Suleman Ahmad Tudu ya fitar, ta bayyana cewa asusun na daga cikin sharuɗɗan shirin RAAMP mai samun tallafin bankin Duniya.

A cewar gwamnatin jihar, an kirkiro shirin ne domin samar da kuɗaɗen gyara da kula da hanyoyin karkara, tare da inganta harkokin sufurin noma a yankunan karkara.

Sabon Darakta Janar ɗin, Bashir Abdullahi Gusau, ya shafe sama da shekaru 30 yana aiki a ɓangaren kula da harkokin kuɗi a gwamnatin jihar Zamfara.

Ya taɓa riƙe muƙamai da suka haɗa da Akanta na Jiha da Daraktan Albashi a ma’aikatar kuɗi ta jihar, kafin ritayarsa a watan Disamban 2025 daga ofishin Sakataren gwamnatin jihar.

Bashir Abdullahi Gusau na da digirin MBA daga Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, sannan memba ne a ƙungiyoyin ƙwararru daban-daban.

Gwamna Lawal ya buƙaci sabon shugaban asusun da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya tare da amfani da ƙwarewarsa wajen bunƙasa ayyukan more rayuwa a jihar Zamfara.

Aminu Dahatu/Gusau

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara