Labarai
An Bukaci ’Yan Jarida Su Kiyaye Ɗabi’un Aiki
Ƙungiyar ‘Yan Jarida reshen jihar Nasarawa ta sake jaddada aniyarta ta ƙara wa mambobinta ƙwarewa domin su yi gogayya da takwarorinsu na duniya ta hanyar amfani da fasahar basirar na’ura wato AI cikin aikin jarida yadda ya dace.
Da yake jawabi a wani taron horaswa na kwana ɗaya da aka gudanar a Lafiya, shugaban ƙungiyar na jihar, Kwamared Salihu Muhammad Alkali, ya bayyana horaswar a matsayin wani mataki na tabbatar da cewa ’yan jarida a jihar sun kasance masu gogayya da kuma sahihanci a aikinsu.
A cewarsa, kayan aikin da ake amfani da su shekaru goma da suka gabata ba za su wadatar ba a wannan zamani, yana mai cewa fasahar AI ta daina kasancewa tatsuniya, domin yanzu tana taimakawa wajen rubuta kanun labarai da tantance bayanai.
Ya ƙara da cewa wajibi ne ’yan jarida su rungumi amfani da AI domin ƙara saurin aiki da tabbatar da gaskiyar bayanai, musamman wajen yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, wanda Babban Mataimakinsa kan Harkokin Jama’a, Peter Ahemba ya wakilta, ya bayyana AI a matsayin takobi mai kaifi biyu, yana mai cewa tana da anfani amma kuma tana da haɗari idan ba a yi amfani da ita yadda ya dace ba.
Ya ce duk da cewa AI na iya gudanar da ayyuka cikin sauri, har yanzu mutum ne ke da ikon tafiyar da fasahar.
Ahemba ya yaba wa shugabannin ƙungiyar NUJ bisa shirya taron, yana mai cewa gwamnatin jihar na ɗaukar matakai domin ganin al’ummar Nasarawa sun ci gaba da tafiya da zamani a fannin fasaha.
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Bunƙasa Fasahar Cikin Gida sun horas da matasa 100 kan AI da nazarin bayanai a makon da ya gabata.
Sakatariyar dindindin ta ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu ta jihar, Hajiya Hadiza Dahiru, ta hannun Daraktan Yaɗa Labarai Musa Abdullahi Ogoshi, tare da shugabannin kafafen yaɗa labarai, sun buƙaci ’yan jarida su kiyaye ɗabi’un aiki da alhakin da ya rataya a wuyansu.
Masana da suka gabatar da muƙalu a taron sun yi jawabi kan batutuwa daban-daban da suka haɗa da tasirin AI a aikin jarida na zamani da kuma rawar aikin jarida wajen rage tashin hankali a lokacin siyasa.
Sun jaddada bukatar kafafen yaɗa labarai su rika amfani da dandamalinsu wajen kwantar da tarzoma tare da inganta aikin jarida mai nagarta.
Wasu daga cikin mahalarta taron, Esther Enna ta Precious FM Lafia da Abubakar Abdullahi na Daily Trust da Charity Ashiki ta NTA, sun yaba wa shugabannin NUJ bisa shirya horaswar.
Kimanin ’yan jarida 80 daga sassa daban-daban na jihar ne suka halarci taron ƙara wa juna sani.
Aliyu Muraki/Lafia
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
