Labarai
An Bukaci Mata Da Matasa Su Shiga Siyasa
Jam’iyyar ADC ta buƙaci mata da matasa a Najeriya su fito su shiga harkokin siyasa domin bayar da gudunmawa wajen cigaban ƙasa.
Shugaban matasan jam’iyyar na ƙasa, Kwamared Balarabe Rufai, ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai, inda ya ce jam’iyyar ta buɗe ƙofofinta ga matasa tare da rage kuɗin sayen fom domin ƙarfafa musu guiwar tsayawa takara.
Ya kuma buƙaci ’yan Najeriya su kwantar da hankalinsu kan rikice-rikicen shari’a da ke gaban jam’iyyar, yana mai cewa shugabannin ADC na ƙoƙarin magance matsalolin.
A nata ɓangaren, mai neman takarar gwamnan jihar Legas a ƙarƙashin ADC, Princess Abiodun Islamiyyatu, ta yi alƙawarin aiwatar da kaso 35 cikin 100 na wakilcin mata a dukkan matakan gwamnati idan ta samu nasara.
Sauran masu neman takara daga jihohi daban-daban sun buƙaci mata da matasa su haɗa kai tare da amfani da damar zaɓe wajen zaɓar shugabanni nagari domin kawo sauyi da cigaba a ƙasa.
Sun kuma jaddada cewa cikakken shiga siyasa daga mata da matasa na da muhimmanci wajen samar da ci gaba mai ɗorewa da kare muradun al’umma.
Bashir Mayere/Abuja
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
