Kasuwanci
Gwamna Namadi Yasha Alwashin Bunkasa Jihar Jigawa
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce gwamnati ta sanya jihar a cikin wani tushe na farfado da tattalin arziki da wadata cikin shekara daya da ta gabata.
Gwamnan ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa al’ummar jihar domin cika shekara guda a kan karagar mulki.
Ya ce, shekara daya da ta wuce an rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar Jigawa, kuma a yau suna bikin cika shekara guda na sadaukar da kai da aka samu da ci gaba.
Malam Umar Namadi ya ci gaba da bayanin cewa, a cikin shekarar da ta gabata, gwamnatin da ke ci yanzu ta taba rayuwar dubban mutane ta hanyar inganta tattalin arzikinsu, ayyukan daukar ma’aikata da tsare-tsaren inshorar lafiya.
Sauran sun hada da kara samar da abinci tare da ayyukan noma da kuma inganta ababen more rayuwa.
Ya ce, wadannan nasarorin na nuni ne da jajircewarsu wajen kyautata rayuwar al’ummar jihar.
“Ina mika godiyata ga ‘yan majalisar zartarwa ta jiha, ‘yan majalisar jiha, ma’aikatan shari’a, masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gidan gwamnati.”
A cewarsa, yayin da suke yin la’akari da wadannan nasarori, sun yi alkawarin ci gaba da yi wa jiharsu da al’ummarta hidima da sadaukarwa da.
KARSHE/USMAN MZ/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
