Connect with us

Labarai

MaJalisar Kasa Za Ta hukunta Jami’an Gwamnatin Da Basa Karbar Gayyatar Ta

Published

on

Majalisar wakilai za ta sanyawa Ministan Muhalli da Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) takunkumi idan har suka kasa amsa gayyatar kwamitinta kan muhalli a zama na gaba.

 

Takunkumin da aka shirya yi wa masu rike da mukaman gwamnati ya biyo bayan gazawar da suka yi wajen bayyanawa da kuma gabatar da jawabai game da batutuwan da suka shafi zaizayar guguwa, ambaliyar ruwa da kwararowar hamada a yawancin al’ummomi a fadin kasar.

 

Da yake jawabi shugaban kwamitin Mista Pondi Gbabojor, ya nuna rashin jin dadinsa da halinsu na minista da kuma shugaban hukumar NEMA inda ya jaddada cewa wannan ne karo na biyu da suke yin watsi da gayyatar tare da tabbatar da cewa ba za a sake amincewa da irin wannan hali ba.

 

Don haka shugaban kwamitin ya umurci magatakardar kwamitin da ya rubuta wa dukkansu biyun domin isar da damuwar kwamitin.

 

“Maladimi ya aika wasika ga ma’aikatar muhalli da NEMA tare da bayyana rashin jin dadin kwamitin domin wannan shi ne karo na biyu da ba su bayyana ba kamar yadda kwmaitin ya bukata”, inji shi.

 

Ya ce an shirya taron ne domin nemo hanyar da za a bi wajen magance illolin da zaizayar ke haifarwa a al’ummomi daga jihohin Anambra shida, Bayelsa, Delta, Legas, da Ondo da kwararowar hamada a Kano da ambaliyar ruwa a jihar Bauchi.

 

A jawabin da ya gabatar a gaban kwamitin babban daraktan hukumar kula da ganuwar koren itatuwa na kasa Dr Yusuf Maina Bukar, ya shaidawa kwamitin cewa kariya da dashen itatuwa akai-akai shi ne kadai mafita ga munanan yanayi na zaizayar kasa da kwararowar hamada a Najeriya.

 

Dokta Maina Bukar ya kuma tabbatar da cewa, wayar da kan al’umma kan muhimmancin dashen itatuwa da kuma hadarin sare bishiyu zai taimaka wajen habaka albarkatun makamashin al’umma.

 

Ya kuma ba da tabbacin hukumar ta kudiri aniyar kare busasshiyar kasa ta hanyar ajandar kawo sauyi na gwamnati mai ci a kan samar da abinci da habaka tattalin arziki.

 

COV: TSIBIRI/Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara