Labarai
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Ya Bukaci Musulmi Su Ci Gaba da Darussan Ramadan
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin tunani a kan darussan sadaukarwa, tausayi, juriya da kuma kyakkyawan fata, yayin da gwamnati ke ƙoƙarin magance ƙalubalen da ƙasa ke fuskanta.
A cikin saƙon Sallah da babban sakataren yaɗa labaransa, Levinus Nwabughiogu ya fitar, mataimakin kakakin ya tabbatar da cewa majalisar na ci gaba da ƙuduri wajen aiwatar da dokoki da za su inganta rayuwar ‘yan Najeriya.
Ya kuma buƙaci mabiya addinin Musulunci da su ci gaba da bin koyarwar Annabi Muhammad (SAW), tare da ƙara yawan addu’o’i domin samun haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa.
Mataimakin kakakin, wanda ya taya Musulmi murnar wannan lokaci na farin ciki, ya roƙi Allah da Ya karɓi dukkan ibadunsu da sadaukarwar da suka yi, tare da shiryar da shugabanni da al’umma gaba ɗaya zuwa kyakkyawar makoma.
Salihu Tsibiri/Abuja
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
