Kasuwanci
Majalisar Wakilai Zata Dauki Mataki Akan Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba
Majalisar Wakilai za ta kaddamar da yakin kawo karshen Hakar Ma’adinai ba bisa ka’ida ba dake al’ummar kasar asarar sama da dalar Amurka biliyan 9 duk shekara.
Shugaban Kwamitin wucin gadi kan hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, Sanni Abdulraheem, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a lokacin kaddamar da kwamitin a harabar majalisar dokokin tarayya Abuja.
Sanni Abdulraheem, wanda ya jaddada mahimmancin kwamitin ga tattalin arzikin kasa, ya bayyana hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a matsayin wani bala’i da ke gurgunta kudaden shiga na kasa, da rura wutar aikata laifuka, da kuma zubar da muhalli.
Shugaban kwamitin ya bayyana cewa, wani bangare na ayyukan kwamitin na toshe hanyoyin samun kudaden shiga, tabbatar da gaskiya, da kuma tabbatar da cewa arzikin ma’adinan kasa na bayar da gudummawa sosai ga ci gaban tattalin arziki.
“An kiyasta cewa Najeriya na asarar kusan dala biliyan 9 a duk shekara saboda ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, wannan satar albarkatunmu da ya kamata ya ciyar da al’ummarmu ya dade da yawa, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji dan majalisar.
Abdulraheem ya bayar da tabbacin cewa, ta hanyar sa-ido, majalisar za ta karfafa hanyoyin bin diddigin kudaden shiga, da kuma tabbatar da cikkaken alfanun da ake samu daga bangaren ma’adinai na Nijeriya kai tsaye zuwa cikin asusun gwamnati, maimakon wasu tsirarun mutane ne.
Dangane da kamfanin karafa na Ajaokuta, shugaban kwamitin ya koka da cewa, a tsawon shekarun da suka gabata, ba a yi amfani da muhimman kadarorin masana’antu ba, yayin da sauran kasashe ke cin gajiyar irin wannan albarkatun, yana mai jaddada cewa tare da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, da ba a taba yin irinsa ba, za a farfado da masana’antar nan ba da jimawa ba.
Kwamandan hukumar tsaron farin kasa ta civil Defense ya ba da tabbacin cewa hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya za ta baiwa kwamitin goyon baya da hadin kai don ganin an cimma dukkan muhimman harajin.
COV: TSIBIRI
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
