Labarai
Bellingham Ya Zama Gwarzon Wasan La Liga Na Bana
An zaɓi ɗan ƙwwallon Real Madrid, Jude Bellingham a matsayin gwarzon ɗan wasan La Liga na bana a kakar farko da ya yi a Sifaniya.
Bellingham, mai shekara 20, ya ci ƙwallo 19 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, wanda ya taimaka Real Madrid ta lashe kofin bana kuma na 36 jimilla.
Ƙungiyar Santiago Bernabeu ta kare a matakin farko a teburin gasar da tazarar maki 10 tsakaninta da Barcelona ta biyu mai rike da La Liga na bana.
Haka kuma ɗan wasan tawagar Ingila, ya zura ƙwallo hudu a raga a Champions League, inda ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta kai wasan karshe a bana.
RanarAsabar 1 ga watan Yuni Real Madrid za ta fafata da Borussia Dortmund a wasan karshe a gasar ta zakarun Turai.
Tsohon ɗan ƙwallon Dortmund ya yi takarar gwarzon dan wasan La Liga a bana tare da takwaransa, Vinicius Jr da Antoine Griezmann na Atletico Madrid da Artem Dovbyk na Girona da kuma Robert Lewandowski na Barcelona.
Ƙyaftin din ƙungiyoyin dake buga La Liga ne ke yin zaben tare da magoya baya da mahukuntan dake gudanar da ƙyautar.
Bellingham ne ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasan Bundesliga a 2022/23 a lokacin da yake taka leda a Dortmund, daga baya Real Madrid ta dauke shi kan kudi Fan miliyan tamanin da takwas da dubu dari biyar kafin fara kakar da aka kammala.
-
Labarai5 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai6 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai6 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai6 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
-
Labarai3 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
