Connect with us

Labarai

Adalci a Kauru LGA Yayin da Tsarin Raba Mukamai ke Kara Karɓuwa Domin Wakilci Nagari

Published

on

Masu ruwa da tsaki daga masarautun gargajiya na Kumana da Chawai a Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun amince da wani tsarin raba mukamai na siyasa da nufin magance rashin daidaito da aka dade ana fama da shi a yankin.

Wannan matsaya ta samu ne bayan tarurrukan da aka gudanar a ranakun 26 da 27 ga watan Maris, 2026, inda aka gabatar da shawarar juyawar mukamai na siyasa tsakanin manyan rukuni uku na yankin, wato Masarautar Kauru, Masarautar Kumana da Masarautar Chawai.

A karkashin wannan tsari, an ware kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya ga Masarautar Kauru, kujerar Majalisar Dokokin Jiha ga Masarautar Chawai, yayin da kujerar Shugaban Karamar Hukuma aka bai wa Masarautar Kumana.

Masu ruwa da tsaki daga Kumana da Chawai sun yaba da rawar da dattawan al’umma, tsofaffin jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki suka taka a tattaunawar, suna mai cewa wannan mataki wani yunkuri ne na gina hadin kai da zaman lafiya a Kauru.

Sai dai, wannan matsaya ta jawo suka daga wani bangare na masu ruwa da tsaki a cikin jam’iyyar APC a yankin.

Wannan bangare, karkashin jagorancin wani Zakka Peter da S.M. Taggah, ya nuna adawa da tsarin raba mukaman, inda suka goyi bayan sake zaben tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Muktar Zakari Chawai, da kuma dan majalisar dokokin jiha, Haruna Barnabas Danmaigona.

Sun bayyana cewa ya kamata a bar zabin shugabanni ga muradin jama’a ta hanyar dimokuradiyya maimakon tsarin raba mukamai.

A martaninsu, kungiyar KYA, wato  Kauru Youth Ambassadors wanda Junaidu Ishaq Maisalati ke jagoranta ta jaddada cewa tsarin raba mukamai hanya ce halal a dimokuradiyya domin tabbatar da adalci da hana wata kabila ko bangare mamaye iko.

Sun kuma yi nuni da sakamakon zaben 2023, inda suka ce sakamakon ya nuna yadda jama’a ke kallon yadda shugabanci ya gudana a yankin.

KYA ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki a Karamar Hukumar Kauru da su fifita hadin kai da cigaban al’umma gaba daya fiye da muradun bangarori.

Har ila yau, ta bukaci Gwamnatin Jihar Kaduna da ta mara baya ga shirye-shiryen da ke inganta hadin kai da tabbatar da adalci wajen shiga harkokin siyasa.

Kungiyar ta jaddada cewa wannan tsarin raba mukamai shi ne matakin farko na kokarin karfafa dimokuradiyya da tabbatar da daidaitaccen wakilci a Kauru.

Daga: Yusuf Zubairu

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara