Labarai
Hajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa tace ta dawo da ci gaba da bitar maniyyatan aikin hajjin bana a dukkan kananan hukumomin jihar bayan kammala azumin watan Ramadan.
Daraktan Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala ganawa da manyan jami’an hukumar a Dutse babban birnin jihar.
Yana mai cewar, hukumar da dakatar da bitar ne saboda azumin watan ramadan.
A don haka, a zancen da ake yi yanzu, an dawo da bitar maniyyatan gadan-gadan domin kara fadakar da su gami da ilmantar da su yadda za su gudanar da aikin hajji a kasa mai tsarki.
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma bukaci maniyyata da su tashi tsaye wajen ganin sun samu ilimin aikin hajji domin samun damar yin aikin hajji karbabbe.
Yayi nuni da cewar, hukumar ta kammala shirye-shiryen tantance lafiyar maniyyata, wanda hakan ya sanya hukumar aikin hajji ta kasa ta jinjina wa tsarin jihar Jigawan, kuma ta farko wajen yin hakan.
Labbo, ya kara da cewar hukumar za ta yi zama na musamman da shugabannin shiyoyinta na jihar da kuma jami’anta na kananan hukumomi wato center officers domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tsarin fara jigilar maniyatan daga nan gida zuwa ƙasa mai tsarki.
Ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi, bisa goyon bayan da yake ba su domin ganin jihar ta ci gaba da zama ta ɗaya a gudanar da aikin hajji.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai22 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
