Connect with us

Labarai

NSAP ta haɗa kai da Sojoji domin magance rikicin manoma da makiyaya a Najeriya

Published

on

Ƙungiyar Sarrafa dabbobi ta kasa ta bayyana cewa haɗin gwiwa da rundunar sojin Najeriya na da muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin da suka haɗa da matsin lamba kan tsarin samar da abinci, ƙaruwar rashin tsaro a yankunan karkara, da kuma rikice-rikicen manoma da makiyaya da ke shafar kiwon dabbobi a ƙasar.

Shugaban ƙungiyar, Farfesa Olaniyi Babayemi, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a gabanin taron shekara-shekara na 51 na NSAP da aka gudanar a Kaduna.

Farfesa Babayemi ya bayyana cewa an kafa NSAP tun a shekarar 1973 da nufin inganta kiwon dabbobi, ƙarfafa tsarin abinci, da tallafawa ci gaban ƙasa ta hanyar hanyoyin kimiyya.

Ya ce rundunar soji, ta hanyar kasancewarta a yankuna daban-daban, tare da ƙarfin jigila da tattara bayanan tsaro, za ta iya taimakawa wajen kare hanyoyin kiwo, kare al’ummomin karkara, da kuma tallafa wa tsarin kiwo na zamani.

Ya jaddada cewa wannan haɗin gwiwa ba nufin soja zai mamaye harkar noma ba ne, illa samar da yanayi mai aminci da zai bai wa noma da kiwo damar bunƙasa.

A cewarsa, ci gaban kiwon dabbobi mai ɗorewa a Najeriya na dogara ne da zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma.

Ya ƙara da cewa, “Hanya mafi dacewa ita ce rungumar tsarin zamani kamar kiwon dabbobi a gona (ranching), sarrafa kiwo, da inganta abinci ga dabbobi. Waɗannan matakai na rage rikici tare da ƙara yawan amfanin gona da dabbobi.”

Shugaban ya kuma yi kira ga al’ummomin noma da kiwo a faɗin ƙasar da su zauna lafiya da juna.

Ya ce: “Ci gaban noma da zaman lafiya dole ne su tafiya tare. Ba za mu iya samun tsaro mai ɗorewa ba idan babu zaman lafiya a matakin al’umma.”

Farfesa Babayemi ya ce taron na nufin fito da shawarwari masu amfani da za su taimaka wajen inganta kiwon dabbobi, rage rikice-rikice, da ƙarfafa zaman lafiya a ƙasa.

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Farfesa Philip Anthony Vantsawa, ya ce wannan shi ne karo na farko cikin fiye da shekaru 50 da aka shirya taron a NDA wato Kwalejin Horasda Hafsoshin Soja ta Nigeria dake Kaduna.

Ya ce taron zai ba masu ruwa da tsaki damar tattaunawa kai tsaye da rundunar soji domin nemo mafita mai ɗorewa ga rikicin manoma da makiyaya da ke addabar ƙasar.

Farfesa Vantsawa ya ƙara da cewa za a fitar da sanarwar ƙarshe (communiqué) domin gwamnati ta yi amfani da ita wajen tsara manufofi na magance matsalar.

Taken taron shi ne: “Haɗin Kan Soja da Fararen Hula Domin Ci Gaban Kiwon Dabbobi Mai Dorewa da Tsaron Ƙasa.”

Usman Sani

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara