Labarai
Kiristoci a Kwara sun fito kan titi domin bikin Palm Sunday
Dubban mabiya addinin Kirista a jihar Kwara sun fito kan tituna domin bikin Palm Sunday, ranar tunawa da shigowar Yesu Almasihu cikin birnin Urushalima cikin nasara, kamar yadda littattafan addini suka bayyana.
Bikin na kuma nuni da ƙarshen azumin kwanaki 40 na Lenten Fast da kuma fara makon ibada na Easter (Holy Week).
Mabiya addinai daga dariku daban-daban sun taru a Cocin Saint Barnabas Cathedral, Sabo-Oke, inda daga nan suka gudanar da jerin gwanon tafiya na sa’o’i da dama ta wasu muhimman titunan birnin Ilorin, ciki har da Murtala Way, Maraba, Amilegbe, Ipata, Opo-Malu, Emir’s Road, Taiwo Isale, Unity da kuma yankin Ofishin Wasiƙa, kafin daga bisani su koma cocin inda aka kammala da addu’ar rufewa (benediction).
Da yake jawabi bayan kammala jerin gwanon, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kwara, Right Reverend Sunday Adewole, ya bukaci Kiristoci da su ci gaba da kasancewa cikin tsayuwar imani da hidima ga Allah.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙoƙari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, yana mai cewa tsaron jama’a ya kamata ya kasance abu na farko a fifiko.
Adewole ya kuma jaddada tasirin hauhawar farashin man fetur da ƙarancin wutar lantarki a gidaje da kasuwanci, yana mai cewa akwai bukatar gaggawar magance waɗannan matsaloli na tattalin arziki.
A nasa ɓangaren, Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda wakilinsa, Reverend Timothy Akangbe, ya halarta, ya bukaci jama’a da su ci gaba da yin addu’a domin ci gaban jihar da Najeriya baki ɗaya.
Ya kuma jaddada muhimmancin tawali’u da soyayya a rayuwar yau da kullum.
Tsohon Sakatare na CAN, Pa Olusola Ajolore, ya yi kira da a ɗauki matakan gaggawa wajen magance matsalar tsaro, tare da shawartar gwamnatoci su yi amfani da kuɗaɗen tsaro yadda ya kamata domin kare rayuka da dukiya.
Ya kuma bukaci samar da ayyukan yi da kuma sake duba kundin tsarin mulki domin dacewa da halin da ake ciki a yau.
Haka kuma, Babban Annabi Segun Korode na Cocin Cherubim and Seraphim Movement Church, Hedikwatar Ilorin, ya tunatar da mabiya cewa su riƙa gode wa Allah a kowane lokaci tare da koyi da tawali’un Yesu Almasihu wanda ya zo da ceton ɗan adam.
Bikin Palm Sunday a Ilorin ya nuna haɗin kai na ibada tare da ƙara jaddada kira ga al’umma kan zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki.
Ali Muhammad Rabiu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
