Labarai
Nasarawa Ta Umarci Kamfanin Hakar Ma’adinai Ya Fice Daga Wurin Aiki
Gwamnatin jihar Nasarawa ta umarci kamfanin Ideal Mines Company da ya dakatar da dukkan ayyukan hakar ma’adinai nan take tare da ficewa daga wurin aikin da ke ƙauyen Endo a yankin Udege, ƙaramar hukumar Nasarawa.
Kwamishiniyar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta jihar, Dakta Margaret Elayo, ce ta bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a garin Lafia.
Ta ce matakin ya biyo bayan gazawar kamfanin wajen bin yarjejeniyar da aka cimma da gwamnati, duk da cewa an sha tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma la’akari da rahotannin tsaro.
Ta ƙara da cewa gwamnati ta riga ta taɓa dakatar da ayyukan kamfanin, sai dai ya garzaya kotu domin neman umarnin hana matakin, amma kotun tarayya da ke Lafia ta yanke hukunci a goyon bayan gwamnati.
A cewarta, umarnin gwamnati na yanzu ya tanadi cewa kamfanin ya kwashe dukkan kayansa, injina, motoci da ma’aikata daga wurin cikin ƙayyadadden lokaci.
Dakta Elayo ta ce matakin na cikin manufofin gwamnati na tabbatar da bin doka wajen hakar ma’adinai, da tabbatar da zaman lafiya a yankunan da ake aiki, tare da kare muradun al’umma.
Ta ce gwamnati za ta tura jami’an tsaro domin tabbatar da cikakken bin wannan umarni da kuma hana duk wani aiki ba tare da izini ba a wurin.
A cewarta, gwamnatin Nasarawa na ƙoƙarin gyara tsarin harkar ma’adinai domin ya amfani da al’umma kai tsaye ta hanyar samar da damar aiki da ci gaban tattalin arziki.
Ta kuma buƙaci masu ruwa da tsaki da su kasance masu bin doka da oda yayin da ake ci gaba da aiwatar da gyare-gyare a ɓangaren ma’adinai a jihar.
Aliyu Umar Muraki/Lafia
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
