Labarai
An Ceto Yaro Dan Watanni 19 Da Ake Zargin Cin Zarafinsa A Kano
Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman ta jihar Kano ta ceto wani jariri mai watanni 19 mai suna Musa, bayan zargin cin zarafi da sakaci daga mai kula da shi.
An ceto yaron ne bayan korafe-korafe daga mazauna unguwar Tsamiya Babba, inda suka kai rahoto ga hukumomi kan halin da ake ciki na yaron da ake zargin yana fuskantar cin zarafi duk da cewa an ba mai kula da shi riƙonsa bisa doka daga Nassarawa Children’s Home.

Binciken farko ya nuna cewa yaron na fama da rashin isasshen abinci, sannan ana kulle shi shi kaɗai a gida na tsawon lokaci yayin da mai kula da shi ke fita harkokinta.
Mazauna yankin kuma sun ce yaron na yawan kasancewa cikin haɗari ba tare da kulawa ba, har ma yana wasa da kaji ba tare da kulawar manya ba, lamarin da ke barazana ga lafiyarsa.
Kwamishiniyar ma’aikatar, Amina Abdullahi, ta kai ziyara kai tsaye domin duba halin da ake ciki, inda ta umurci tawagar musamman ta ma’aikatar tare da Nassarawa Children’s Home su gudanar da cikakken bincike.
Binciken da aka gudanar ya gano cewa matar da ke kula da yaran, Aisha Shuaibu, tana da yara biyu a hannunta daga gidan marayu, ciki har da Musa mai watanni 19.
Rahotanni sun ce ta amince da barin yaron shi kaɗai sau uku, amma ta gaza bayar da gamsasshen bayani kan wasu raunika da aka gano a jikinsa.

Daga bisani an mika lamarin zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta Gezawa domin ci gaba da bincike, yayin da ake tsare da wacce ake zargi.
Kwamishiniyar ta yi kakkausar suka kan cin zarafin yara, tana mai gargadin cewa ma’aikatar za ta ɗauki matakin gaggawa kan duk mai kulawa da yara da ya aikata irin wannan laifi.
Ta ƙara da cewa za a ƙara sa ido da kai ziyara gidajen kula da yara a faɗin jihar domin tabbatar da tsaro da jin daɗin yaran da ke cikin kulawa.

Khadijah Aliyu/Kano
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
