Labarai
Sojojin Najeriya sun wayar da kai kan shirin inshorar ma’aikata a Kaduna
Sojojin Najeriya sun jaddada ƙudirinsu na inganta walwala da tsaron kuɗi ga jami’ansu ta hanyar shirye-shiryen jin daɗi da kariya.
Darakta-Janar na Hukumar harkokin kudi ta sojoji, Manjo Janar Julius Osifo, ne ya bayyana hakan yayin wani taron wayar da kai kan shirin inshorar sojoji da sauran shirye-shiryen walwala da aka gudanar a hedikwatar Runduna ta Ɗaya a Kaduna.
Ya ce wannan shiri na daga cikin ƙoƙarin da ake yi domin tabbatar da cewa jami’an soja da iyalansu sun fahimci dukkanin tallafin da aka tanada musu domin kariya da walwala.
Osifo ya ce shirin ya dace da manufar Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa wadda ke nufin ƙarfafa rundunar soja ta zama mai ƙwarewa, juriya da kuma shirye-shiryen kare ƙasa, tare da ingantattun tsare-tsaren walwala.
Ya bayyana wasu daga cikin muhimman shirye-shiryen da suka haɗa da inshorar ma’aikata, sashen kula da kuɗaɗen ba na gwamnati ba, da kuma shirin bankin microfinance na sojoji.
A cewarsa, waɗannan tsare-tsare na ba sojoji damar samun inshorar rayuwa, lamunin kuɗi cikin sauƙi da kuma sauran hidimomin kuɗi ga sojoji, tsofaffin sojoji da kuma al’ummomin da ke kusa da su.
Ya ƙara da cewa idan soja ya rasa ransa wajen hidimar ƙasa, sojoji suna ci gaba da biyan albashi da alawus ga iyalansa na tsawon shekaru biyu domin rage musu wahala.
A nasa jawabin, Kwamandan Runduna ta Ɗaya, Manjo Janar Abubakar Sadiq Wase, ya bayyana taron a matsayin mataki mai muhimmanci da ke shafar jin daɗi da kuma ingancin aikin soja.
Wakilin sa, Birgediya Janar Sherif Aremu, ya ce sanin waɗannan tsare-tsare na ba sojoji ƙwarin gwiwar yin aiki cikin kwanciyar hankali, tare da sanin cewa an kare iyalansu.
Ya kuma yaba wa Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa da NAFIC kan ƙoƙarin zamani wajen inganta tsarin inshora ta hanyar fasahar zamani da sauƙaƙa hanyoyin amfani da shi.
Taron ya samu halartar jami’an soja daga sassa daban-daban na Runduna ta Ɗaya a Kaduna.
Suleiman Sani/Kaduna
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
