Connect with us

Labarai

Zaben 2027: NNPP Ta Sha Alwashin Maye Gurbin Tinubu da Radda

Published

on

Daga Isma’il Adamu

Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar lashe karin mukaman siyasa a zaben shekarar 2027, ciki har da na shugaba kasa da gwamnan Jihar Katsina.

Sabon shugaban jam’iyyar da aka rantsar a Jihar Katsina, Alhaji Armaya’u AbdulKadir ne ya bayyana haka a zaben shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a Katsina.

Ya ce jam’iyyar, wacce ta ba da muhimmanci ga ilimi, walwalar jama’a, karfafa matasa da ci gaban abubuwan more rayuwa, ta kara samun farin jini a wajen jama’a saboda ingantaccen jagoranci da wakilcin da take bayarwa ta hannun mambobinta da ke rike da  mukamai a matakin kananan hukumomi, jihohi da tarayya.

Masu zabe sun ga abin da jam’iyyarmu ke aiwatarwa. ‘Yan majalisa da sauran wadanda aka zaba suna aiki a matakai daban-daban tun daga kananan hukumomi har zuwa matakin tarayya. ‘Yan Najeriya sun shaida kwarjininmu, shi ya sa muke da tabbacin lashe karin kujeru a zaben 2027.

Jagoranmu na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kuduri aniyar karbar shugabancin kasa, yayin da a nan Jihar Katsina kuma muke shirin tsayar da kwararru masu kwarewa da kuzari da za su iya lashe kujerar Gwamna da sauran mukaman zabe.”

AbdulKadir, wanda ya jaddada cewa NNPP na kara samun karbuwa a tsakanin ‘yan Najeriya, ya ce hakan ya nuna a kwanan nan ta hanyar sauya sheka da wasu ‘yan wasu jam’iyyu suka yi zuwa NNPP. Ya kuma bukaci mambobin jam’iyyar da su kara samun magoya baya domin tunkarar zaben 2027.

Zaben shugabannin jihar, wanda ya samar da mambobi 38 ta hanyar maslaha, ya samu kulawar INEC da hukumomin tsaro, tare da halartar wakilan jam’iyyar daga kasa da yankin Arewa maso Yamma, da kuma daruruwan mambobin jam’iyyar.

Alhaji Armaya’u AbdulKadir ya  kasance Shugaban jam’iyya, Sani Arga mataimaki na farko, Tijjani Zakari sakatare, Umar Musa sakataren shirya ayyuka, sannan Hauwa Abubakar ta zama shugabar mata.

Tunda farko, shugaban kwamitin gudanar da taron, Alhaji Muhammad Yusuf-Fagge, ya yaba wa wakilai da mambobin jam’iyyar a jihar bisa ladabi da natsuwar da suka nuna a yayin taron, da kuma yadda suka amince da hanyar maslaha wacce “ta sauƙaƙa aikin.”

Ya yi kira ga mambobin jam’iyyar a jihar da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai, biyayya da ladabi, tare da kara yawaita mambobi da samun goyon baya ga jam’iyyar a jihar.

Labarai

Labarai2 hours ago

NHIA Ta Fara Daukar Jami’an Kula da Lafiya na Ƙasa a Jigawa

Usman Muhammad Zaria  Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) ta fara aikin daukar Jami’an Kula da Lafiya na...

Labarai7 days ago

Baragurbi a Aikin Jarida na Barazana ga Sahihancin Kafafen Yada Labarai – Shugaban NUJ-FRCN

Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), reshen FRCN Kaduna, Kwamared Umar Adamu Sarkinfada, ya bayyana cewa mummunan aikin jarida...

Labarai2 weeks ago

Ƙaruwa a Shan Abubuwan Sha Masu Ƙara Ƙarfi na Haddasa Damuwar Lafiya a Kano

Abubuwan sha masu ƙara ƙarfi, waɗanda aka fi sani da energy drinks ko energizers, na ƙara samun karɓuwa a faɗin...

Labarai2 weeks ago

Shugaba Tinubu Ya Taya CPSO Usman Shugaba Murnar Cika Shekara 45 da Haihuwa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Kwamishinan ‘Yan Sanda, Usman Musa Shugaba, wanda shi ne Babban Jami’in Tsaron ‘Yan...

Labarai2 weeks ago

TSARO: Gwamnan Jihar Neja Ya Nuna Alhini Kan Harin ‘Yan Ta’adda a Al’ummomin Borgu

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa kan harin ‘yan ta’adda da aka kai wa wasu...

Labarai2 weeks ago

Allah Ya Jikan Jarman Kauru Da Ke Jihar Kaduna

Mun sami labarin rasuwar tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Kaduna, Malam Suleiman Lawal Jarman Kauru. Malam Suleiman Lawal, mai shekaru...

Labarai2 weeks ago

Gwamnatin Kano Ta Faɗaɗa Damar Tattalin Arziki ga Mata da Masu Buƙata Ta Musamman

An kammala kasuwar baje kolin mata ta tsawon kwanaki huɗu, wadda Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara da Masu Buƙata Ta Musamman...

Labarai2 weeks ago

Rundunar Tsaro Ta Haɗin Gwiwa Ta Hallaka ’Yan Bindiga 150

Rundunar tsaro ta haɗin gwiwa da ta ƙunshi Sojojin Nijeriya, Hukumar Tsaron Farin Ciki (DSS), ’Yan Sanda da sauran hukumomin...

Ilimi2 weeks ago

Gwamnatin Neja Ta Amince da Sake Buɗe Makarantun Gwamnati da Masu Zaman Kansu daga 12 ga Janairu

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya amince da sake buɗe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a faɗin...

Ilimi2 weeks ago

Gwamnatin Nasarawa Ta Roki Malaman Jami’o’i Masu Yajin Aiki Su Koma Aji – SSA Ahemba

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta yi kira ga malaman manyan makarantu mallakar jihar da ke yajin aiki da su janye yajin...

Mafi Shahara