Labarai
ASUU-SSU Ta Zargi VC Da Kary Dokokin Jami’ar Jihar Sakkwato
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Sakkwato (ASUU-SSU), ta zargi Mataimakin Shugaban Jami’ar (Vice-Chancellor) da kin bin umarnin Gwamnan Jihar Sakkwato game da sauke Bursar da ya kai lokacin ritaya.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a Sakkwato a ranar Litinin, 8 ga Disamba 2025, ƙungiyar ta ce Gwamna Dr. Ahmed Aliyu Sakkwato, wanda shi ne Visitor na Jami’ar, ya amince da buƙatarsu na tabbatar da bin dokokin Jami’ar ta hanyar amincewa da ritayar Bursar ɗin.
ASUU-SSU ta bayyana cewa Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Sakkwato ya aika da takardar umarni mai lamba HS/ADM/101/VOL-1, ɗauke da kwanan wata 18 ga Nuwamba 2025, wadda ta umurci Bursar ya miƙa ragamar ofis ga jami’in da ya fi kowa girma a sashen Bursary, har sai an naɗa sabon Bursar bisa tanadin dokar Jami’ar Jihar Sakkwato ta 2009.
Sai dai ƙungiyar ta ce kusan wata guda ke nan VC ɗin bai aiwatar da umarnin ba.
Shugaban reshen ASUU-SSU, Kwamared Bello Musa, ya bayyana cewa sun rubuta wa VC takardar tunatarwa da wata takarda ta biyu, amma ba su samu amsa ba.
Haka kuma, sun gudanar da taro biyu da shi, amma ya dage cewa akwai wata amincewa da Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi ta jihar ta bayar a 2024 game da matsayin Bursar.
Sai dai ASUU ta ce wannan hujja “ba ta da tushe”, domin sabon umarnin Gwamna “ya fi ƙarfi kuma ya shafe duk wani tsohon matsayi”, musamman ma ganin cewa Bursar ya kai lokacin ritaya tun 3 ga Oktoba 2024.
A cewarta, Ma’aikatar Kula Da Ma’aikata ta riga ta aika masa da takardar ritaya ta hannun Ma’aikatar Kudi ta jihar.
Ƙungiyar ta ce ci gaba da bari tsohon ma’aikaci ya rattaɓa hannu kan muhimman takardun Jami’a “na karya doka, kuma na tauye ikon Jami’a (University Autonomy).”
ASUU-SSU ta yaba wa Gwamnan jihar bisa “ƙarin nuna biyayya ga doka da buɗe ƙofar sauraron ƙorafe-ƙorafe”, tare da buƙatar ya tabbatar da cewa ba a katse hanyoyin isar da sahihan koke-koke zuwa gare shi ba.
Ƙungiyar ta ce zanga-zangar lumana da ta gudanar a Jami’ar na nufin matsa wa VC lamba ya aiwatar da umarnin Gwamna ba tare da ɓata lokaci ba, domin tabbatar da zaman lafiya da daidaiton aiki.
Ta kuma sha alwashin ɗaukar “mataki mafi tsauri” idan ba a aiwatar da umarnin ba.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
