Labarai
Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin Jihohi Shidda
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohi shidda daga sassan ƙasar a ci gaba da tattaunawar da ake yi domin ƙarfafa batun tsaro a ƙasa.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo, Umar Namadi na Jigawa, Nasir Idris na Kebbi, Ahmed Ododo na Kogi, Lucky Aiyedatiwa na Ondo, da Ahmed Aliyu na jihar Sokoto.

Taron, wanda ya ɗauki kusan mintuna 40, ya mayar da hankali ne kan muhimman matsalolin tsaro da ke shafar jihohinsu, duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanai ba.
Wakilin Rediyon Najeriya da ke fadar shugaban kasa ya ruwaito cewa wannan zaman na daga cikin kokarin shugaban kasa na ƙara haɗin kai da jihohi wajen magance matsalolin tsaro.

Wannan cigaban ya biyo bayan nasarar da Gwamnatin Tarayya ta samu na kubutar da dalibai 100 da aka yi garkuwa da su a Jihar Neja, baya ga wanda aka yi a Jihar Kebbi.
Ci gaba da irin waɗannan tattaunawa na shugaban kasa na nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin ƙasar.
-
Labarai7 days agoGwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Gina Hanyar Kilomita 95 A Tsafe Don Ƙarfafa Ayyukan Tsaro
-
Labarai5 days agoGwamnatin Jigawa Za Ta Kafa Cibiyar Ayyukan Noma Da Samar Sa Kayayyakin Zamani
-
Labarai7 days agoƊan Takarar Gwamnan Accord A Kebbi Ya Yi Alƙawarin Ƙara Albashin Ma’aikata Zuwa N500,000
-
Labarai7 days agoGwamna Kefas Ya Zargi Jami’an Gwamnatinsa Da Taimaka Wa Haƙar Ba Bisa Ka’ida Ba
-
Labarai5 days agoGwamnatin Jigawa Ta Amince Da Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Miliyoyin Naira
-
Labarai7 days agoUNILORIN Ta Zama Ta Farko A Najeriya Wajen Ingancin Bincike
-
Labarai5 days agoGwamnatin Jigawa Za Ta Biya Diyar Naira Miliyan 982 Ga Wadanda Aikin Hanya Ya Shafa
