Kasuwanci
Kasashen Afirka Na Taro Kan Ta’addanci A Abuja

An buɗe taron yini biyu kan yaƙi da ta’addanci a ƙasashen Afirka da ke gudana a Abuja, babban birnin Najeriya.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya ƙaddamar da taron mai taken ‘ƙarfafa ayyukan haɗin kai tsakanin ƙasashe da bunƙasa hukumomi don murƙushe ta’addanci’.
An shirya taron domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci a tsakanin ƙasashen nahiyar Afirka ta hanyar haɗin kai na sojoji da daƙile kwararar makamai da kuɗade tsakanin ƙasashen da zummar tallafa wa masu aikata manyan laifuka.
Taron na zuwa ne yayin da ƙasashen Afirka da dama ke fuskantar barazanar tsaro daga ƙungiyoyin masu iƙirarhin jihadi da ƴan bindiga musamman a sassan yankin Sahel.
Shugabanin ƙasashe daga yankin da masana kan harkoki tsaro daga nahiyar da ɓangaren majalisar ɗinkin duniya ne za su halarci taron.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
