Connect with us

Labarai

Kotu ta Tsare Mutum 29 da Ake Zargi da Fafutukar Kafa Kasar Yarabawa

Published

on

Kotun majistre ta Iyaganku da ke Ibadan ta bayar da umarnin a tsare mutum 29 da ake zargin masu fafutukar kafa ƙasar Yarabawa ne saboda yadda suka yi wa harabar sakatariyar jihar Oyo ƙawanya.

A ranar Laraba ne aka gurfanar da mutanen saboda zargin su da hannu a harim da suka kai kan sakatariyar da kuma ofishin gwamna da bai yi nasara ba.

A baya-bayan nan ne wasu mutane da suka rufe fuskarsu suka yi dirar mikiya a sakatariyar jihar inda suka kafa tutarsu kafin jami’an tsaro su tarwatsa su.

A cewar jaridar Vanguard, mutanen waɗanda ke fuskantar tuhume-tuhume bakwai kan haɗa baki da cin amanar ƙasa da kuma shiga haramtacciyar ƙungiya da riƙe makami cikin jama’a da kuma aikata abin da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba.

Mutanen da ake zargi, har da wata matashiya da manyan mata biyar, an tsare su a gidan gyaran hali da ke Ibadan bisa umarnin babban majistare, Olabisi Ogunkanmi.

Daga bisani kuma mai shari’ar ya ɗage sauraron ƙarar zuwa 1 ga watan Agusta.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara