Connect with us

Labarai

Ambaliyar Ruwa ta Shafe Manyan Titunan Birnin Dubai

Published

on

 

Ambaliyar ruwa ta rufe manyan titunan birnin Dubai kuma babban filin jirgin samansa ya kasance cikin rudu yayin da cibiyar hada-hadar kudi ta Gabas ta Tsakiya din ta kasance a kulle a ranar Laraba, kwana guda bayan da aka yi ruwan sama mai tsananin gaske da ba a taba irinsa ba.

A kalla mutum daya ya mutu, wani dattijo mai shekaru 70 da haifuwa, a cikin motarsa a Ras Al-Khaimah, daya daga cikin masarautun kasar bakwai masu arzikin man fetur, in ji ‘yan sanda.

An samu katsewar wutar lantarki a kusa da birnin Dubai, wanda ke cike da ambaliyar ruwa da ya nitsar da motocin da aka bari.

An ga irin wannan al’amuran a kusa da yankunan da suka hada da Sharjah, makwabciyar Dubai, inda mazauna yankin suka yi ta ratsa manyan tituna tare da kai komo a cikin kwale-kwale na wucin gadi.

“Wannan shi ne lamari mafi muni da na taba fuskanta,” in ji wani dan kasar Dubai mai shekaru 30, wanda ya so a sakaya sunansa, bayan wata tafiyar tsawon mintuna 15, ya koma sa’o’i 12 a kan tituna da ambaliyar ruwa ta mamaye.”

“Na san cewa idan motata ta lalace zata nutse ni ma kuma zan nutse da ita.”

Makarantu za su ci gaba da kasancewa a rufe a Dubai har zuwa mako mai zuwa, in ji hukumomi, wanda ke nuna irin wahalar tsaftace muhallin.

A halin da ake ciki, ayyuka suna yi tafiyar hawainiya a filin jirgin sama na Dubai, mai tasha mafi yawan zirga-zirgar jiragen sama a duniya, yayin da ma’aikatan suka kasa isowa aiki sakamakon ambaliyar ruwa, sannan kuma aka dakatar da akasarin motocin zirga-zirgar jama’a.

Yayin da aka jinkirta kusan kowane jirgi akai-akai, an gaya wa fasinjoji su nisanci filin “sai dai idan ya zama dole,” in ji ma’aikatan Filin jirgin saman Dubai.

An kuma jinkirta tashin jirage da dama, an soke da kuma karkatar da su a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Talata, lokacin da jiragen suka ce su na yunkurin tashi cikin ruwa mai zurfi.

Guguwar ta afka wa kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain ne da daren jiya litinin da kuma ranar Talata bayan da a baya suka afka wa kasar Oman, inda mutane 19 suka mutu ciki har da kananan yara.

Maryam Al Shehhi, babbar jami’ar hasashen yanayi a cibiyar nazarin yanayi ta UAE, ta musanta rahoton da ke cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi shukar gajimare inda ta fesa sinadarai don kara yawan ruwan sama.

VOA

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai3 hours ago

An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa  ta samar da katafaren masauki  kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah...

Labarai2 days ago

Kungiyar AFAN Ta Shirya Taron Bita Ga Manoman Jihar Jigawa

Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa da cibiyar binciken yanayin kasa dake Kaduna sun shirya wa manoma daga...

Fasaha3 days ago

An Bukaci Gwamnatin Sakkwato Ta Agaji Jami’ar Jihar

Kungiyar Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato ASUU-SSU ta yi kira ga gwamnatin Jihar ta duba halin da kungiyar ke ciki da...

Kasuwanci3 days ago

Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe – KANUPDA

  Manajan Daraktan Hukumar Tsare-tsare da Ci gaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Architect Ibrahim Yakub Adamu ya yi gargadin...

Ilimi3 days ago

Zamu Zuba Jarin Dala Miliyan 600 a Nijeriya – Mr. Robert

Shugaba Kasa Bola Tinubu ya samu masu zuba jarin dala miliyan 600 daga kamfanin sufurin jiragen ruwa na kasar Denmark,...

Labarai5 days ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi5 days ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai1 week ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Ilimi1 week ago

Daliban Jihar Kebbi Da Ke Kasashen Waje Za Su Sami Tallafin Naira Miliyan 309

Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da kashe sama da Naira miliyan Dari Uku da Tara, domin biyan tallafin karatu na...

Kasuwanci1 week ago

Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano

Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma...

Mafi Shahara