Connect with us

Labarai

EFCC Ta Ayyana Neman Yahaya Bello Ruwa A Jallo

Published

on

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati EFCC ta ayyana tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na sada zumunta mai ɗauke da hoton tsohon gwamnan.

Matakin hukumar na zuwa ne ’yan awanni bayan kotu ta ɗage sauraron ƙarar da hukumar ta shigar saboda wanda take zargin bai halarci zaman kotun ba.

Yayin zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan EFCC, Kemi Phinro ya faɗa mata cewa “wani mutum da ke da kariya daga tuhuma ne ke bai wa tsohon gwamnan mafaka.
Sanarwar ta kuma buƙaci duk wani mai bayani game da inda tsohon gwamnan yake ya gaggauta kai mata rahoto ko ofishin ’yan sanda mafi kusa.
Tun a jiya Laraba rahotanni suka ce gwamnan Kogi na yanzu, Usman Adodo ne ya fice da Yahaya Bello a motarsa lokacin da jami’an EFCC suka yi wa gidansa tsinke a Abuja.

Kawo yanzu dai Gwamnatin Kogi ba ta ce komai ba game da zargin.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai12 hours ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Bada Lamunin Sama Da Naira Biliyan 3 Ga Hukumar Alhazan Jihar

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da bukatar hukumar Alhazai ta jihar na naira biliyan uku da miliyan dari...

Labarai14 hours ago

An Tsinci Gawar Wani Mutum A Cikin Rijiya A Karamar Hukumar Gezawa

Al’ummar kauyen Babawa da ke karamar hukumar Gezawa a Kano sun shiga cikin firgici bayan da aka tsinci wani mutum...

Labarai2 days ago

Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Ta Samar Da Masauki Na Alfarma Ga Alhazan Jihar

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce ta samar wa Alhazan Jiha katafaren masauki na alfarma  a kusa...

Labarai3 days ago

Hukumar Alhazai Ta Kasa Ta Sanar Da Kudin Aikin Hajjin Bana

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da kudin aikin Hajjin shekarar 2025. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa...

Labarai3 days ago

Sanata Yari Ya Bada Gudummawar Kudi Ga Wadanda Harin Sama Ya Shafa A Maradun

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’azeez Yari Abubakar, ya bayar da naira miliyan 23 da kuma buhuna 105 na kayan abinci...

Ilimi3 days ago

Gwamna Namadi Tare Da Hadin Gwiwar Kasar Qatar Sun Samar Da Cibiyar Bunkasa Ilimi A Jigawa

Gwamna Mallam Umar Namadi ya kaddamar da Cibiyar Al’amuran  Addinin Musulunci a kauyen Babbar Riga dake karamar hukumar Malam-Madori a...

Labarai3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Jajantawa Al’ummar Jihar Neja Bisa Iftila’in Fashewar Tankar Mai

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana alhininsa kan fashewar tankar mai da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da 80 tare...

Labarai4 days ago

Gwamnatin Neja Ta Haramtawa Motocin Da Suka Fito Daga Hanyar Maje Bin Gadar Dikko

Gwamnatin Jihar Neja ta ba da umarnin hana motocin da suka  fito daga Maje hawa gadar Dikko. Gwamnan jihar Mohammed...

Labarai5 days ago

Hukumar Shige da Fice Ta Gargadi Jama’a Kan Sabuwar Kungiya Achad Life Mission

Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta bayyana damuwa kan bullar wata sabuwar kungiya mai suna Achad Life Mission...

Labarai5 days ago

Majalisar Dattijai Ta Bukaci Karfafa Jarin Bankin Lamunin Gidaje Na Tarayya

Majalisar dattawan na shirin yin amfani da bangaren zartaswa na gwamnati kan gaggauta samarda kwakkwaran jari ga babban bankin bayar...

Mafi Shahara