Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Published

on

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu.

Jakadan Qatar a Najeriya Dr.  Ali Bn Ghanem Al-Hajari, ya yi wannan alkawarin  a yayin bikin kaddamar da ginin sabuwar makarantar firamare a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Ya bayyana cewa ilimi na da matukar muhimmanci wajen farfado da jihar da rikuci ya daidaita.

Jakadan wanda ya kaddamar da ginin tare da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya jaddada cewa  idan aka kammala  za a  samar da kayan aiki na zamani don baiwa marayu damar koyo a kyakkyawan yanayi.

Gwamnatin Qatar za ta bayar da muhimmin tallafi ga marayu kusan 1000 a jihar Borno, za mu kuma ba da muhimmanci ga shirin gwamnati na samar da ingantaccen yanayin koyo ga yaran da rikicin Boko Haram ya daidaita.” Inji Ghanem.

Tunda farko Ambasada Ali Bn Ghanem Al-Hajari da mukarrabansa sun kai ziyarar ban girma ga Gwamna Babagana Zulum a fadar gwamnati inda ya sake jaddada aniyar kasarsa na taimakawa jihar Borno.

Gwamna Zulum ya nuna jin dadinsa ga gwamnatin Qatar bisa tallafin tare da ba da tabbacin samar da yanayi mai kyau don samun ilimi mai inganci.

A watan Janairun bana ne gwamnan ya aza harsashin ginin gidan marayu da kungiyar agaji ta Qatar Charity Organisation ta gina.

Jakadan ya samu rakiyar mataimakinsa, Mista Abdullah Hilal Alnuimi, da daraktan kungiyar agaji ta Qatar Hamdi Abdou.

 

Dauda Iliya

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara