Connect with us

Ilimi

Gwamnatin Borno Za Ta Kashe Naira Biliyan Daya Don Horar Da Malaman Makarantu

Published

on

Gwamnatin Jihar Borno ta amince da kashe naira miliyan dubu daya domin horar da malaman makarantun firamare a fadin kananan hukumomi ashirin da bakwai na jihar.

Gwamna Babagana Zulum ya amince da hakan ne a lokacin da yake kaddamar da sabbin sakatarorin ilimi na kananan hukumomi da aka nada a Maiduguri.

Ya yi nuni da cewa sama da malamai dubu daya da ke da takardar shaidar kammala karatun sakandare za su kara samun horon da zai ba su damar samun karancin cancantar koyarwa.

Horon zai hada da malaman da ba su da kwarewar koyarwa amma an gano cewa za su iya ba da horo bisa bayanan gwajin cancantar da aka yi musu,” in ji Zulum.

Gwamnan ya bukaci sabbin sakatarorin ilimi da aka nada da su maida hankali akan aikinsu, inda ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da gazawa za a maye gurbinsa.

Na umurci mai girma kwamishinan ilimi da ya ba ni rahoto kan ayyukan kowace sakatariyar ilimi. Za a maye gurbin wadanda suka kasa cimma bukatun gwamnati,” in ji Zulum.

Kwamishinan ilimi, kimiya, fasaha da kirkire-kirkire, Lawan Wakilbe, ya ce mutane 126 ne suka nemi wannan matsayi kuma bayan kammala jarrabawar tantancewa, an zabo ashirin da bakwai bisa ga kwazon da suka yi.

A halin da ake ciki, Gwamna Babagana Zulum ya bayar da motocin  hamsin da takwas ga sakatarorin ilimin  da jami’an sa ido a fadin kananan hukumomi ashirin da bakwai da ke jihar.

 

Dauda Iliya

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai7 hours ago

Amurka Ta Dakatar Da Kudurin Kai Jirgin Bama-Bamai Zuwa Isra’ila

Amurka ta sanar da batun dakatar da shirin ta na kai jirgi dauke da bamabamai zuwa Israila a cikin makon...

Labarai8 hours ago

NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido...

Kasuwanci1 day ago

CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati

Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan  Yulin 2024 ga masu POS su kammala rajista...

Fasaha1 day ago

Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno

  Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin horas da malamai 1,949 a matakin farko da aka gano cewa suna iya...

Fasaha1 day ago

Bankuna Za Su Fara Cirar 0.5% Daga Masu Tura Kudi Ta Intanet

  Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci bankunan kasar su fara cirar kaso 0.5 cikin 100 na duk kuɗin da...

Labarai1 day ago

An kashe Falasɗinawa 34,800 tun fara yaƙi – Ma’aikatar lafiyar Hamas

Ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe Falasdinawa 34,789 a yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba,...

Ilimi4 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin...

Labarai5 days ago

An Samar Da Sabon Tsari Da Zai Inganta Harkar Noman Rogo A Najeriya

Shugaban kungiyar masu noman rogo ta Najeriya (NCGA), Mustapha Othman Bakano, ya kaddamar da wani tsari na samar da kasuwa...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai6 days ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Mafi Shahara