Connect with us

Labarai

NAHCON Ta Jinjinawa Hukumar Alhazai Ta Jihar Jigawa Bisa Shirye-shiryen Hajjin Bana

Published

on

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo ya karbi tawagar gani da ido daga Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON domin tantance ayyukan hukumar.

A jawabin shugabar tawagar kuma  babbar jami’ar  hukumar ta NAHCON a jihar Jigawa Hajiya Rabi’atu Dahiru Nyako, ta bayyana cewa manufar ziyarar ita ce tantance kayayyakin aikin hukumar tare da duba yaddatake gudanarda shirye-shiryen aikin Hajjin bana.

Tawagar za ta tantance kayan aiki, da shirye-shiryen jigilar maniyyatan jihar, da takardun tafiya kasa mai tsarki, da fasfo fasfo da sauransu”.

Babbar Jami’iar ta bayyana gamsuwa da irin shirye-shiryen da hukumar ta yi.

 

A nasa jawabin, babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana cewa, an samu nasarori da dama a kan shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin shekarar 2024 a jihar.

Shugaban hukumar ya kara da cewa, hukumar ta kara wa’adin  gudanar da lakcocin aikin hajji ga maniyyatan da ke fadin kananan hukumomi ashirin da bakwai na jihar.

Ya nanata kudurin gwamnatin jihar na tabbatar da jin dadin Alhazan  Jigawa tun daga gida Najeriya har zuwa kasar Saudiyya.

Labbo ya yabawa NAHCON bisa ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai ga hukumar domin samun nasarar aikin Hajjin na bana.

Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, tawagar ta duba sashin amfani da na’ura mai kwakwalwa, da ayyukan da ake gudanarwa, tare da wasu  gine-gine da aka gyara, da  sauran kayayyakin zamani na hukumar.

Usman Muhammad Zaria

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai3 hours ago

Ma’aikatan Ceto Na Cigaba Da Neman Jirgin Shugaban Kasar Iran Da Ya Bace

Da yammacin yau lahadi ne tarin ma’aikatan ceto suka bazama wajen aiki gano jirgi mai saukar ungulu dauke da shugaba...

Labarai3 days ago

Majalisar Dattijan Na So A Bai Wa Kananan Hukumomi Yancin Kai

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda...

Labarai3 days ago

‘Yan Ƙwadago Sun Yi Watsi Da N48,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

  Ƙungiyar Ƙwadago NLC ta yi fatali da tayin naira 48,000 da Gwamnatin Tarayya ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin...

Labarai3 days ago

Tinubu Zai Ciyo Bashin $500m Don Sayen Mitocin Lantarki

  Majalisar Dattawa ta sahale wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciyo bashin Dala miliyan 500 da nufin samar da mitocin...

Ilimi4 days ago

Za A Fara Daukar Masu Sakamakon Jarabawar NECO A Jami’o’in Birtaniya

  Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO. Shugaban hukumar shirya...

Labarai4 days ago

Jirgin Farko Na Alhazan Najeriya Ya Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki

A yau Laraba 15 ga watan Mayun 2024 ne jirgin Najeriya na farko ya tashi da Alhazan Jihar Kebbi 423...

Labarai4 days ago

Najeriya Ta Kaddamar da Shafin Intanet Don Samun Bayanai Game da Ma’adinai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet ranar Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai...

Labarai5 days ago

Tsohon Lauyan Trump Ya Ce Ubangidansa Ya Ba ‘Yar Fina-finan Batsa Toshiyar Baki

Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da kara su ka yi ta fatan ya...

Labarai5 days ago

Kotu Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Zaman Gidan Yari Na Watanni 2 Bisa Satar Doya

Kotun Majistare da ke Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani mutum mai suna Isah Sani hukuncin...

Labarai5 days ago

Jamhuriyar Benin Ta Haramta Fitar Da Masara Zuwa Nijar

Jamhuriyar Benin ta hana fitar da masara zuwa ƙasashen waje a daidai lokacin da farashin hatsi ya yi tashin gwauron...

Mafi Shahara