Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Ta Bada Tallafin Littattafan Ilmantar Da Alhazai Aikin Hajji

Published

on

Gwamnatin Jihar Jigawa ta baiwa hukumar jin dadin Alhazai ta jihar da kuma hukumar kula da ilimin addinin musulunci gudunmawar kwafin litattafai dubu biyar mai suna “GUZURIN MAHAJJATA” da nufin karfafawa maniyyata ilimi da shirye-shiryen tafiya kasa  mai tsarki.

Da yake mika littattafan ga shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai da Babban Sakatare na Hukumar Ilimi ta Musulunci, Alhaji Ahmed Umar Labbo da Dokta Mubarak Abdulwahab Hassan, Sakataren Gwamnatin Jiha, Malam Bala Ibrahim ya ce wannan karimcin na daga cikin kudirin gwamnatin jihar na  don sauƙaƙa tafiya da gudanar da aikin Hajjin cikin sauki ga Mahajjatan jihar.

Malam Bala Ibrahim ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na samar da dukkanin abubuwan da suka dace ga maniyyatan.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yanke shawarar daukar nauyin buga kwafin litattafai guda 5,000 domin karfafawa maniyyata ilimi da kuma shirye-shiryen tafiyarsu kasa mai tsarki.

A jawabinsa, shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya gode wa gwamnati bisa wannan karimcin.

Shugaban, wanda Daraktan Yada Labarai na Hukumar Malam Murtala Abdu Babura ya wakilta, ya yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa  bayar da tallafin Naira miliyan daya ga Alhazan jihar.

A lokacin da yake bitar littafin, Malam Mahmud Yunusa ya bayyana cewa littafin yana da matukar muhimmanci ga Jagorar aikin hajji, inda ya ce  yana da kyau Alhazan  su karanta shi, da ma  masu son koyon Fiqhu da ladubban aikin Hajji.

Malam Mahmud Yunusa ya yabawa marubucin littafin aikin, tare da godewa Gwamna Umar Namadi bisa jajircewarsa na ci gaba da kyautata jin dadin alhazai a kowane lokaci.

Usman Muhammad Zaria

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai10 hours ago

Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Tarakta 300 Ga Manoma Daga Amurka

A kokarinta na ci gaba da habbaka harkokin noma, Gwamnatin Jihar Jigawa ta ƙulla wata yarjejeniyar haɗin gwiwa da wasu...

Labarai10 hours ago

An kama masu zanga-zanga 17 a jami’ar Texas

An sake kama ƙarin mutanen da ke da alaƙa da zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasɗinawa inda a wannan karon...

Labarai23 hours ago

An Samar Da Masauki Kusa Da Harami Ga Alhazan Jihar Jigawa

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa  ta samar da katafaren masauki  kusa da Masallacin Harami da ke birnin Makkah...

Labarai3 days ago

Kungiyar AFAN Ta Shirya Taron Bita Ga Manoman Jihar Jigawa

Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa da cibiyar binciken yanayin kasa dake Kaduna sun shirya wa manoma daga...

Fasaha4 days ago

An Bukaci Gwamnatin Sakkwato Ta Agaji Jami’ar Jihar

Kungiyar Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato ASUU-SSU ta yi kira ga gwamnatin Jihar ta duba halin da kungiyar ke ciki da...

Kasuwanci4 days ago

Mun Aika Musu Takardun Gargadi Kafin Ginin Ya Rushe – KANUPDA

  Manajan Daraktan Hukumar Tsare-tsare da Ci gaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), Architect Ibrahim Yakub Adamu ya yi gargadin...

Ilimi4 days ago

Zamu Zuba Jarin Dala Miliyan 600 a Nijeriya – Mr. Robert

Shugaba Kasa Bola Tinubu ya samu masu zuba jarin dala miliyan 600 daga kamfanin sufurin jiragen ruwa na kasar Denmark,...

Labarai6 days ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi6 days ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai1 week ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Mafi Shahara