Labarai
‘Yan Sanda Sun Ceto Yara Mata 28 Da Aka Sace A Katsina
Rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro sun ceto ‘yan matan nan 28 da aka sace daga kauyen Kasai da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq ya sanya wa hannu, ta ce an kubutar da dukkan ‘yan matan ba tare da wani rauni ba.
‘Yan fashin sun yi wa yaran ‘yan shekara takwas zuwa sha biyar kwanton bauna ne a bayan gari, inda suka je dibar itacen da za su kai gida domin yin girki.
Sanarwar ta ce da samun rahoton faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Abubakar, ya tura jami’ai zuwa dajin tare da yin tattaki domin ceto yaran.
Ya yi bayanin cewa ‘yan bindigar sun yi watsi da yaran ne sakamakon matsin lamba da ‘yan sanda suka yi musu, inda suka gudu suka bar yaran wadanda a halin yanzu suke cikin koshin lafiya.
“Kokarin hadin gwiwa da tawagar ceto ta sa kai, tare da dabarun da rundunar ta dauka, ya sa aka sako dukkan wadanda aka sace”. Inji shi.
“Wannan nasara ta nuna jajircewar rundunar da kuma duk wanda ke da hannu acaiki.n ceton.
Sanarwar ta kara da cewa “Za a ci gaba da kokarin tabbatar da tsaron al’umma da jihar baki daya.
Ismai’l Adamu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
