Connect with us

Kasuwanci

Hukumar Kwastam Ta Mayar Da Tirela 6 Na Kayan Abinci Da Ta Kwace A Katsina

Published

on

Hukumar kwastam ta mayar da Tirela shidda na buhunan abinci da ta kama a Kongolam da ke kan iyakar Katsina da Jamhuriyar Nijar a a karamar hukumar Maiaduwa ta jihar Katsina.

Wannan dai ya yi dai-dai da umarnin shugaban kasa kamar yadda shugaban hukumar kwastam ta Nijeriya, Bashir Adeniyi ya sanar yayin wata ganawa da ya yi da al’ummar yankin iyakar Kongolam a karshen mako.

A lokacin da yake mika motocin guda shida dauke da hatsi a ofishin hukumar kwastam da ke Katsina, shugaban hukumar shiyar Jihar Katsina, Muhammad Umar, ya bayyana cewa an saki buhunan abincin ne ga masu su da sharadin cewa za a sayar da su a kasuwannin Najeriya kawai.

Ya ce jami’an hukumar kwastam sun kwace kayayyakin ne domin aiwatar da dokar hana fitar da kayayyakin abinci da shigo da su daga kasashen waje saboda karancin abinci da hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a kasar a halin yanzu.

Kwanturola Umar ya umarci masu wadannan kayayyakin su kasance masu kishin kasa tare da bin ka’idar siyar da kayan abinci a cikin Nijeriya a matsayin hanyar da za ta ci gaba da kokarin tabbatar da wadatar abinci.

Ya kuma kara da cewa, jami’an hukumar tare da hadin gwiwar jami’an Leken asiri da tawagar rundunar hadin gwiwa da ke sintiri a kan iyakokin kasar nan za su sa ido , domin tabbatar da cewa ba a fitar da wadannan kayayyakin daga kasar nan ta barauniyar hanya ba.

Kwanturolan na yankin Katsina ya kuma roki jama’a da su bayar da bayanan da za su taimaka wajen dakile safarar kayayyakin abinci da haramtattun kayayyaki daga kasar nan.

A jawabinsa yayin mika kayayyakin, shugaban kwamitin kula da samar da abinci na jihar Katsina, Jabiru Tsauri, ya gargadi masu safarar kayayyaki da masu motocin da aka sako da su bi umarnin shugaban kasa ta hanyar sayar da hatsin a kasuwannin Najeriya kawai.

Isma’il Adamu

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai15 hours ago

Gini Ya Fado Kan Mutane 11 A Kano

Wani gini ya fado kan ma’aikata suna tsaka da aikin gini a unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a...

Ilimi17 hours ago

Gwamnatin Qatar Za Ta Tallafa Wa Marayu 1000 A Borno

Gwamnatin Kasar Qatar ta yi alkawarin tallafawa kimanin marayu dubu daya da rikicin Boko Haram ya rutsa da iyayensu. Jakadan...

Labarai3 days ago

Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar...

Ilimi3 days ago

Daliban Jihar Kebbi Da Ke Kasashen Waje Za Su Sami Tallafin Naira Miliyan 309

Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da kashe sama da Naira miliyan Dari Uku da Tara, domin biyan tallafin karatu na...

Kasuwanci3 days ago

Kwari Masu Lalata Amfanin Gona Sun Mamaye Gonakin Tumatur A Kano

Shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano, AFAN, Abdullahi Maibreadi, ya bukaci gwamnati a dukkan matakai da su taimaka wa manoma...

Fasaha3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Shirin Bada Bashin Kayyaki Ga ‘Yan Kasa

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ƙaddamar da kashin farko na tsarin karɓar bashin kaya ga ƴan ƙasar. Bayanin hakan na...

Labarai3 days ago

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Rufe Bankin UBA Kan Kin Biyan Haraji

Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta raufe rassan bankin UBA kan kin biyan harajin Naira miliyan 14....

Labarai4 days ago

Mutum Biyar Sun Mutu Cikin Kwale-Kwalen ƴan Ci-Rani

Mutum biyar har da yaro sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake hanyar ruwa da ta ratsa Ingila da safiyar...

Kasuwanci4 days ago

CBN Ya Sake Karya Farashin Dala Zuwa N1,101

Babban Bankin Nigeria CBN ya sake sanar da matakin karya farashin dala daga N1,251 zuwa N1,101. CBN ya bayyana haka...

Ilimi4 days ago

Ƴan Sanda Za Su Yi Bincike Kan Makarantar Leads British

Rundunar ƴan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta ce ta aika tawagar jami’anta zuwa makarantar Leads British bayan bidiyon...

Mafi Shahara