Labarai
Mutum Biyar Sun Mutu Cikin Kwale-Kwalen ƴan Ci-Rani
Mutum biyar har da yaro sun mutu yayin da suke ƙoƙarin tsallake hanyar ruwa da ta ratsa Ingila da safiyar ranar Talata, in ji hukumomin Faransa.
Masu gadin teku sun ce mutanen da lamarin ya rutsa da su na koƙarin zuwa Birtaniya ne cikin wani kwale-kwale maƙare da ƴan ci-rani 110.
Tuni aka ƙaddamar da aikin ceto domin zaƙulo mutanen da suke cikin ruwa.
Sakataren harkokin cikin gida na Birtnaiyam James Cleverly ya ce: “Dole ne a magance wannan bala’i. Ba zan amince da halin da ake ciki ba da ke janyo asarar rayuka.”
Mista Cleverly ya ce gwamnatin Birtaniya tana yin duk mai yiwuwa na kawo ƙarshen miyagu masu safarar mutane.”
Tun farko, majalisar dokokin Birtaniya ta amince da ƙudirin neman tura masu neman mafaka a Birtaniya zuwa Rwanda bayan shafe watanni ana ƙiƙi-ƙaƙa a kai.
Kudurin ya ayyana Rwanda a matsayin kasar da ba ta da wata matsala dangane da ƙudurin, bayan da kotun ƙolin Birtaniya ta zartar a watan Nuwamba cewa shirin na gwamnati ya saba doka.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
