Ilimi
Daliban Jihar Kebbi Da Ke Kasashen Waje Za Su Sami Tallafin Naira Miliyan 309
Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da kashe sama da Naira miliyan Dari Uku da Tara, domin biyan tallafin karatu na kasashen waje ga ‘yan asalin jihar da ke karatu a Indiya da Masar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Ahmed Idris ya rabawa manema labarai, ta ce kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Alhaji isah Abubakar-Tunga ne ya bayyana hakan a ofishinsa.
Kwamishinan ya ce za a bada Naira miliyan 228 ga dalibai 63 da ke karatu a Indiya, yayin da daliban da ke Kasar Masar za su sami Naira miliyan 81 da dubu 400.
“Haka kuma nan ba da dadewa ba za a bada irin wannan tallafin ga sauran daliban da ke kasashen waje su 50.”
Ya bayyana cewa, a watan Fabrairun 2024, jihar ta biya dukkan daliban jihar da ke karatu a manyan makarantun da ke fadin Najeriya tallafin karatu.
Abdullahi Tukur
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
