Kasuwanci
Hukumar Kwastam Shiyar Jihar Kebbi Ta Sake Bude Kan Iyakar Najeriya Da Nijar
Sabon Shugaban Hukumar Kwastam a Jihar Kebbi, Kwanturola Iheanacho Ernest Ojike, ya bi umarnin Shugaban Hukumar na kasa Bashir Adewale Adeniyi, na sake bude kan iyakar Kamba don ci gaba da hada-hadar kasuwanci a kasashen duniya.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Mohammed Tajuddeen Salisu ya fitar, ya ce Kamba babbar kan iyaka ce mai matukar mahimmanci, da ke samar da kudaden shiga a jihar Kebbi.

Sanarwar ta bayyana cewa, sake bude kan iyakokin zai kara fadada kasuwanci ta halastacciyar hanya da za su yi tasiri wajen gina kasa da inganta tattalin arziki, yana mai cewa hakan ba ya nufin cewa za a yi sakaci ta yadda wasu za su yi amfani da wannan damar wajen shigo da haramtattun kayayyaki da za su yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da kuma kawo cikas ga tsaron kasa ba.
Kwanturolan na jihar ya ce, jami’an hukumar a shirye suke don yin aiki bisa tsarin doka domin saukaka kasuwanci a kan iyakar Kamba ba tare da wata matsala ba, muddin ‘yan kasuwa sun shigo da halastattun kayayyaki da kuma biyan kudaden da suka dace ga asusun Gwamnatin Tarayya.
Sanarwar ta bayyana cewa, Kwanturola Ernest Ojike yana mai jaddada cewa, har yanzu an haramta fitar da kayan abinci zuwa kasashen waje, bisa la’akari da karancin abinci a kasar.
Abdullahi Tukur
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
