Labarai
Jihar Jigawa Za Ta Fara Allurar Rigakafi Da Bada Unifom Ga Alhazai
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce nan ba da dadewa ba za ta fara gudanar da allurar rigakafi tare da raba jaka da sauran kayayyaki ga maniyyatan aikin Hajjin 2024.
Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga wakilin gidan rediyon Najeriya a hedikwatar hukumar da ke Dutse, babban birnin jihar.
Ya yi bayanin cewa allurar rigakafin ga dukkan maniyyatan jihar na daga cikin sharuddan hukumar Saudiyya na bayar da biza.
A cewarsa, ana sa ran za a fara allurar rigakafi da rarraba kayayyakin a cibiyoyin bitar Alhazai da ke fadin kananan hukumomin jihar ashirin da bakwai.
Ya kara da cewa, ana ci gaba da gudanar da taron bita ga Maniyyata a dukkan cibiyoyin da aka kebe a fadin jihar.
Ya ce, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta kammala dukkan shirye-shiryen jigilar Alhazan jihar zuwa kasa mai tsarki cikin sauki.
Ya kuma bayyana cewa hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ce ta tsara jigilar maniyyatan jihar ta bana, inda ta bai wa kamfanin Max Air damar jigilar Maniyyatan jihar zuwa kasar Saudiyya.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai23 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
