Labarai
Gwamna Namadi Zai Biya Tallafin Naira Miliyan 1 Ga Kowani Mahajjaci
Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya amince da biyan tallafin Naira miliyan daya ga kowane mahajjaci daga jihar don yin aikin Hajjin bana a karkashin hukumar jin dadin alhazai ta jihar.
Shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar jigawa, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga gidan rediyon Najeriya a Dutse babban birnin jihar.
A cewarsa, Gwamnan ya dauki matakin ne dangane da karin kudin Hajji da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta yi a baya-bayan nan wanda aka alakanta shi da rashin daidaiton farashin canji.
“Akwai mutanen da suka rigaya suka biya gaba daya, amma kwatsam sai aka samu karin kudin aikin Hajji, karin kudin aikin Hajji babban kalubale ne ga dimbin maniyyata.” Inji shi.

Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Ahmad Umar Labo
Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bukaci dukkan maniyyatan jihar da su tabbatar sun biya sauran kudaden da suka rage wato naira dubu dari tara da goma sha takwas ga hukumar.
Shugaban hukumar ya yi nuni da cewa wadanda za su ci gajiyar tallafin aikin Hajjin su ne wadanda dama sun biya kudin aikin Hajjin ga hukumar.
Idan dai za a iya tunawa, NAHCON ta sanar da karin kudin aikin Hajji da Naira miliyan daya da dubudaritaradagomashatakwas, wanda ya sa adadin kudin aikin Hajji ya kai naira miliyan shuda da dubu dari shida da goma sha bakwai.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
