Kasuwanci
An Fasa Rumbun Abincin Gwamnati A Jihar Kebbi
Wasu mutane sun fasa rumbun abincin gwamnati a Jihar Kebbi da ke Unguwar Bayan Kara a Birnin Kebbi a ranar Lahadi.
Mutanen da suka fasa rumbun sun yi galaba ne a kan jami’an tsaron da ke tsare da rumbun na gwamnati.
An bayyana cewa bayan Rumbun Gwamnati da aka fasa, mutanen sun wawushe kayan abincin da ke makare a wata mota da ta lalace a kan hanya.
Shugaban ’yan kasuwar Bayan Kara dake Birnin Kebbi Muhammadu Gwadangwaji ya ce, ba Rumbun Gwamnati kadai mutane suka fasa ba.
A cewarsa, an fasa wasu shagunan ’yan kasuwa an kuma cinna wa wasu wuta, duk da irin ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi.
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris; Ahmed Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici”.
Ya bayyana cewa: “Tun da farko an samu wasu ɓata-gari sun kai hari kan kayan abinci da Dangote ya aiko jiharmu domin rabawa jama’a sannan suka garzaya ma’ajiyar gwamnati inda nan ma suka kwashe wasu kayan abincin.
“Irin wannan lamari bai taba faruwa a Kebbi ba. Kayayyakin abincin da suka wawashe na daga cikin kayan abincin da gwamnatin jihar ta siya domin raba wa al’umma“.
Ya ce, gwamnati ta ɗauki matakin kare ma’ajiyar ta domin hana afkuwar irin haka anan gaba.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
