Ilimi
Kebbi Ta Zuba Biliyoyin Naira Don Saukaka Rayuwar ‘Yan Kasa – Inji Kwamishinan Yada Labarai

Gwamnatin Gwamna Nasir Idris a jihar Kebbi, yace sun kashe biliyoyin kudade daga ranar 29 ga watan Mayu, 2023 don rage dimbin radadin da al’ummarta ke fama da su, tare da juya dukiyoyin jihar fiye da yadda ya gada.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, wanda ya bayyana haka a taron manema labarai da ma’aikatar yada labarai da al’adu ta shirya, ya jaddada cewa, Gwamnan ya yi nasarar kawo sauyi a Jihar Kebbi ta bangarori daban-daban na rayuwar dan Adam.
“Misali, matsalar da al’umma ke fama da su a halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki, Gwamnan ya sayi hatsi iri-iri na sama da Naira biliyan 12, ya raba wa ‘yan jihar kyauta. Ya kara da cewa, tallafin ya kai ga dukkan nau’o’in jama’ar jihar.
Kwamishinan ya ce, dole ne a yaba wa gwamnatin jihar Kebbi kan yadda ta raba kayan agaji ga kowane fanni na rayuwa, ba tare da la’akari da wata alaka ta siyasa ko addini ba.
Dangane da batun samar da abinci, Kwamishinan ya bayyana cewa, kokari da matakan da gwamnatin Nasiru Idris ta danka sun yi nisa wajen tabbatar da samar da abinci da kuma tabbatar da cewa al’ummar jihar ba su taba fuskantar yunwa ba.
A cewar Kwamishinan, gwamnatin ta kashe makudan kudade wajen siyan kayayyakin amfanin gona iri-iri da kayan aiki tare da raba wa manoman a fadin jihar kyauta baya ga feshin tsuntsayen da ake yi.
Ya kuma yi kira ga ‘yan adawa da masu fafutuka da su daina kamfen din zagon kasa ga gwamnatin Nasiru Idris domin baiwa gwamnan damar mayar da hankali kan ayyukan da jama’a suka zabi shi ya gudanar.
Abdullahi Tukur/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
