Labarai
Akalla Mutane 10 Sun Mutu A Turmutsitsin Karbar Kayan Sallah A Sakkwato

A kalla mutane goma ne suka mutu yayin da wasu da ba a tantance adadinsu ba suka samu raunuka sakamakon turmutsitsin da ya faru a Sokoto.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar, Hassan Sahabi Sanyinna ya fitar, ya ce turmutsitsin ya faru ne sakamakon rashin tsari na rabon kayan abinci da suturar Sallah ga jama’a a unguwar Gawon Nama wanda gida ne na Jagoran jam’iyyar APC mai mulki a jihar, Sanata Alu Magatakardan Wamako.
A cewar sanarwar, wata jami’ar hukumar tsaron farin kaya ta kasa na daga cikin mutane goma da suka mutu a wannan mummunan lamari.
Sanarwar ta mika sakon jaje ga iyalan wadanda suka rasu yayin da suke addu’ar samun lafiya, ga wadanda suka samu raunuka a wurin da lamarin ya faru.
Sannan ta yi kira ga jami’an tsaro su kaddamar da cikakken bincike kan lamarin, da nufin hana sake faruwar haka a nan gaba.
Sanarwar ta kuma bukaci a biya diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wasu da suka jikkata a lamarin.
Hakazalika, sanarwar da wasu jama’a ba su tabbatar ba, sun nuna cewa sama da mutane goma sha biyar ne suka rasa rayukansu a turmutsutsun.
Kokarin da gidan rediyon Najeriya ya yi na tabbatar da faruwar lamarin daga rundunar ‘yan sandan Najeriya da jami’an tsaron farin kaya bai yi nasara ba.
NASIR MALALI/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
