Labarai
Gwamnan Jihar Kebbi Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 75 A Bagudu
Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris, ya kaddamar da aikin gina gidaje guda saba’in da biyar masu dakuna biyu da falo a karamar hukumar Bagudo, da ake ginawa a karkashin shirin Hukumar Kula da Wuraren dake Samar da Wutar Lantarki wato HYPPADEC, na sake tsugunar da wadanda suka rasa gidajensu.
Da yake jawabi a wajen taron a Ganten Fadama da ke karamar hukumar Bagudo, Gwamna Nasir Idris, ya bayyana jin dadinsa da wannan karamcin tare da ba da tabbacin goyon bayan hukumar ta HYPADEC domin cimma manufofinta.
Gwamnan, ya shawarci masu rike da mukaman siyasa da su kyautatawa al’ummarsu ta hanyar gudanar da ayyukan da suka shafi rayuwar al’umma kai tsaye.
A jawabinsa, shugaban hukumar ta HYPPADEC, Alhaji Abubakar Sadiq-Yelwa, ya bayyana cewa, za a gina gidajen ne domin tallafa wa al’ummar jihar musamman mazauna kusa da teku.
Ya ce, daga cikin gidaje 75, za a gina 30 a Ganten Fadama da ke karamar hukumar Bagudo, yayin da za a gina 25 a Tudun Faila na karamar hukumar Shanga sai kuma 20 a karamar hukumar Suru ta jihar.
A cewarsa, hukumar ta yi ayyuka da dama ga al’ummomin da ambaliyar ruwa da gobara ta shafa tare da horar da daruruwan matasa sana’o’i daban-daban domin dogaro da kai.
Abdullahi Tukur
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
