Labarai
Gwamnan Kebbi Ya Bi Sahun Takwarorinsa Na Bada Tallafi Ga Alhazai
Gwamnatin jihar Kebbi ta amince da tallafin Naira miliyan daya ga kowane mahajjacin jihar su dubu uku da dari uku da arba’in da hudu domin sauke farali a aikin Hajjin shekarar 2024.
Kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, biyo bayan taron gaggawa na majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Litinin.
Ya ce, hakan ya biyo bayan karin kudin aikin Hajjin 2024 ne da Naira miliyan daya da dubu dari tara da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta yi.
A cewar sa, za a biya Naira miliyan daya ga kowane maniyyaci da ya kammala biyan kudin aikin Hajjin sa a baya.
Dangane da batun fasa shaguna da sace-sacen hatsi da wasu baragurbi suka yi a babban birnin jihar, Kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar ta yi Allahwadai game da hakan.
Alhaji Yakubu BK ya ce gwamnatin jihar ta yi tir da irin wadannan munanan dabi’u domin ba halayyar mutanen jihar ba ne.
Ya kara da cewa, an kafa kwamiti mai mutum 13 a karkashin jagorancin kwamishinan aikin gona don binciki lamarin.
Kwamitin, zai bankado musabbabin wannan aika-aikar, tare da tantance mutanen da ke da hannu tare da ba da shawarar hanyoyin hana sake aukuwar hakan.
Shima da yake magana akan lamarin, kwamishinan noma da albarkatun kasa, Alhaji Shehu Muazu, ya shaidawa manema labarai cewa, kayan agajin da aka wawashe na gidauniyar Dangote ce ba na gwamnatin jihar ba.
Abdullahi Tukur
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
