Ilimi
An Ceto Daliban Jami’ar Jihar Kogi Da Aka Sace
Jami’an tsaro sun ceto daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi.
Rundunar hadin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro ta ceto daliban su tara ne bayan musayar wuta da ’yan bindigar.
Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta ce a samamen da suka kaddamar a Dajin Osara, yankin da jami’ar take, suka murkushe ’yan bindigar da suka sace daliban.
Sanarwar rundunar ta ranar Lahadi ta ce tserewa ’yan bindigar suka yi suka bar daliban, ganin cewa jami’an tsaron sun fi karkfinsu.
Rundunar ta ce sojoji sun kuma ceto wasu mutane 17 da aka sace a Karamar Hukumar Batsari ta Jihar Katsina.
An ceto mutanen ne bayan daukin da sojoji suka kai inda suka bi sawun ’yan bindigar da suka sace mutanen, suka yi musayar wuta tare da ceto mutanen bayan ’yan bindigar sun tsere.
A Jihar Zamfara ma sojoji sun ceto wasu mutane biyu da aka yi sace a kauyen Danzara da ke yankin karamar hukumar Maru.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
