Ilimi
Dalibai a Jihohin Arewa Maso Yamma Sun Koka Game da Ƙalubalen Tsaro a Yankin
Daga Usman Muhammad Zaria
Daliban makarantu daga jihohin Arewa maso Yamma da suka hada da Kano, Jigawa da Katsina sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su samar musu da tsaro, ingantaccen kiwon lafiya, da taftataccen ruwan sha.
Daliban sun yi wannan kiran ne yayin bikin Ranar Yara ta Duniya da aka gudanar a Kano, wanda Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ta shirya.
Haka zalika ɗaliban sun nemi a mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta domin samun ilimi mai inganci.

Haka kuma, sun buƙaci a aiwatar da dokokin kare haƙƙin yara tare da ba da dama ga daidaito tsakanin jinsi, musamman a fannin ilimin ’ya’ya mata.
Bugu da ƙari, sun koka kan wariyar jinsi, rashin kula da lafiyar ’ya’ya mata yayin al’ada, tare da neman adalci game da cin zarafin yara.
Har ila yau, sun nemi haɗin kai domin inganta walwalar yara a Najeriya a duk matakai.

Yaran sun sake neman goyon bayan kafofin watsa labarai domin yaɗa bukatunsu da kuma tabbatar da samun haƙƙoƙinsu.
A jawabinsa yayin taron, Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Mohammed Farah, ya bayyana cewa UNICEF tana ba da tallafi ga gwamnati wajen magance kalubalen da suka shafi yara.
Ya jaddada cewa domin tabbatar da kowane yaro a Najeriya ya rayu, ya sami ilimi, ya girma cikin mutunci da tsaro, UNICEF na kira ga haɗin gwiwar duk masu ruwa da tsaki domin canja yanayin.

Farah ya tabbatar da kudirin UNICEF na ci gaba da aiki tare da gwamnati, al’umma da ƙungiyoyin farar hula, domin tabbatar da cewa kowane yaro a Najeriya na iya rayuwa, samun ilimi da bunƙasa.
Ya bayyana cewa, tabbas Najeriya ta samu ci gaba, amma akwai buƙatar gaggawa, haɗin kai da ɗorewar aiki domin kare makomar yara.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
