Connect with us

Ilimi

SUBEB da UNICEF Sun Horas da Malaman Firamare a Jigawa

Published

on

Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Jigawa (SUBEB), tare da haɗin gwiwar Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ta horas da malamai kan yadda za su gudanar da gwajin karatu da lissafi ga ɗaliban makarantun firamare.

Mai bada  shawara kan tantance ilimin yara a matakin farko na UNICEF Dakta Farouk Aliyu, ya bayyana cewa horon na kwanaki huɗu wanda ya fara a ranar Litinin, na da nufin tantance matsayin yadda dalibai ke koyon karatu a makarantu.

A cewarsa, sun mayar da hankali ne kan ɗaliban aji ɗaya da aji biyu na firamare da kuma malamansu a fannin lissafi da harshen Hausa a kowace makaranta.

Dakta Farouk Aliyu ya ce manufar wannan shiri ita ce samar da hanya mafi sauki da dalibai za su samu ƙwarewar karatu da lissafi a matakin farko a Jihar Jigawa.

Ya ƙara da cewa, ana kuma son fahimtar yadda malamai ke koyarwa tare da tantance ko suna bin hanyoyin koyarwa da UNICEF da sauran hukumomin ilimi suka koyar.

Ya ce idan aka samu gibi, hakan zai sa a sake horas da malamai da tsara manufofi, ko ma sauya tsarin manhajar karatu gaba ɗaya.

Mashawarcin na UNICEF ya ce an horas da mahalarta 67 waɗanda za su tattara sahihan bayanai masu inganci da za su taimaka wajen tsara manufofin da za su tallafa wa tsarin ilimi a jihar.

UNICEF ta dade tana tallafa wa tsarin ilimi a Jigawa da Najeriya baki ɗaya ta hanyar horas da malamai da samar da kayayyakin koyo da koyarwa.

Wannan horon ya ƙara jaddada ƙudirin Kungiyar Tarayyar Turai da gwamnatin Jihar Jigawa wajen inganta sakamakon koyo tare da tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ƙwarewar karatu da lissafi tun daga tushe.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, an horas da sama da malamai 1,680 na azuzuwan firamare daya zuwa uku, kan hanyoyin koyar da karatu da lissafi  domin inganta koyarwa da samun sakamako mai kyau.

Haka kuma, an raba sama da kayayyakin koyo da koyarwa 152,386 ga ɗaliban matakin farko a makarantun da shirin ya shafa.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara