Connect with us

Labarai

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar da Sabon Ginin Fadar Masarautar Anka

Published

on

Daga Aminu Dalhatu

Gwamna Dauda Lawal ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na dora Jihar Zamfara kan turbar ci gaba mai ɗorewa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da manyan ayyuka a Ƙaramar Hukumar Anka, a wani ɓangare na ci gaba da cika alkawuran yaƙin neman zaɓe da kuma inganta shugabanci a matakin ƙasa.

 

Ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da sake gina Fadar Sarki gaba ɗaya tare da kayayyakin aiki, ƙaddamar da aikin gina titin Anka zuwa Abbare, da gina sabuwar Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Anka, da ofisoshin Hukumar Hisbah da na Rundunar Tsaron Al’umma (CPG), da kuma sake gina Makarantar SAFE da ke Anka.

Da yake jawabi yayin taron, Gwamna Lawal ya buƙaci majalisar masarautar da mazauna yankin su ci gaba da ba gwamnatinsa haɗin kai tare da ɗaukar alhakin kula da sabbin ayyukan da aka ƙaddamar.

Ya bayyana cewa kafin bikin ƙaddamar da ayyukan, ya fara aikin gina titin Anka zuwa Abbare, inda ya bayyana titin a matsayin hanya mai muhimmanci da za ta inganta zirga-zirga zuwa ƙauyuka, ta kuma ƙarfafa harkokin tattalin arziki tare da haifar da bunƙasa ci gaba a yankin.

Gwamna Lawal ya jaddada cewa babu wata al’umma da za ta samu ci gaba ba tare da bin doka da oda ba, inda ya nuna muhimmancin samar da ingantattun ofisoshi ga Hukumar Hisbah da Rundunar Tsaron Al’umma domin su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta fahimci muhimmiyar rawar da cibiyoyin gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba, tare da tabbatar da cewa ayyukan da ake aiwatarwa sun dace da al’adun al’ummomin da abin ya shafa.

 

Gwamnan ya bayyana cewa bayan ƙaddamar da ayyuka a Masarautar Anka da Tsafe , za a gudanar da irin wannan ƙaddamarwa nan ba da jimawa ba a Kauran Namoda da Moriki .

Ya ƙara da cewa ayyukan da ake yi a Bungudu, Bukkuyum, da Zurmi, na tafiya yadda ya kamata, kuma za a kammala su tare da ƙaddamar da su kafin ƙarshen shekarar nan, In Shaa Allah.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara