Connect with us

Ilimi

Majalisar Matan Shugabannin Afirka Ta Karrama Oluremi Tinubu Kan Ayyukan Tallafa wa Mata da Yara

Published

on

Daga Bello Wakili 

Majalisar Matan Shugabannin Kasashen Afirka OAFLAD ta karrama  Uwargidan Shugaban Ƙasar Nijeriya, Oluremi Tinubu  sakamakon gudunmawar da take bayarwa wajen bunƙasa ilimin ‘ya’ya mata.

Karramawar ta kuma yaba da shirye-shiryen da ta aiwatar domin rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai, tare da faɗaɗa tallafin jin ƙai ga iyaye mata da yara a faɗin Nijeriya.

Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa Nana Shettima ce ta wakilci Oluremi Tinubu a babban taron Majalisar ta OAFLAD karo na 29 da na 30 da aka gudanar a Addis Ababa na ƙasar Ethiopia.

OAFLAD, wadda ke aiki ƙarƙashin shirin ta na “We Are Equal”, wato ‘Duk Daya Kuke’, na ci gaba da fafutukar tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata, ƙarfafa tattalin arzikin mata, da inganta samun ilimi a faɗin nahiyar Afirka.

Majalisar ta kuma jaddada buƙatar ƙara haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka domin magance matsalolin da ke addabar mata da yara, musamman a yankunan da rikice-rikice suka shafa.

A jawabinsu  wajen taron, Uwargidan Shugaban Ƙasar Sierra Leone kuma Shugabar OAFLAD, Fatima Maada Bio, tare da Uwargidan Shugaban Ƙasar Ghana, Lordina Mahama, sun yaba wa Sanata Oluremi Tinubu bisa yadda take ci gaba da fafutukar kare haƙƙin mata da yara tare da aiwatar da shirye-shirye masu amfani a Nijeriya da ma wajenta.

Dakta Bio ta jaddada alaƙar da ke tsakanin ci gaba mai ɗorewa da zaman lafiya, inda ta ce ba za a iya tabbatar da cikakken haƙƙin mata ba a wuraren da ke fama da rashin tsaro da rikice-rikice.

Haka kuma, Misis Mahama ta nuna muhimmancin ci gaba da tallafawa ilimin ‘ya’ya mata da kuma ƙarfafa mata masu sana’o’i, a matsayin hanyar gina rayuwa mai ɗorewa.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara