Ilimi
Gwamnati Ta Wajabtawa Dalibai Su Mika “Project” Kafin Aika Su NYSC
Gwamnatin Tarayya ta wajabta wa ɗaliban da suka kammala karatu mika kundin bincikensu na ƙarshe a matsayin sharaɗi kafin a tura su aikin yi wa kasa hidima NYSC.
Dokar za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, 2025, kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya sanar.
Ya bayyana cewa dokar ta shafi duk ɗaliban ajin ƙarshe da suka cancanci zuwa NYSC ko da kuwa a ƙasashen waje suka kammala karatu.
Bisa haka, daga yanzu babu ɗalibin da za sahalewa zuwa NYSC ba tare da ya miƙa takardar shaidar kammala binciken karshe na kammala digirinsa ba.
Gwamnatin Tarayya ta ce hakan zai taimaka wajen yakar matsalar amfani da takardun kammala karatu na bogi da kuma adana ilimi da bincike a ƙasar.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
