Connect with us

Labarai

Manchester United Na Zawarcin Kane, Mainoo Na Son Ya Bar Old Trafford

Published

on

Manchester United na zawarcin dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 32, wanda zai iya barin Bayern Munich a bazara mai zuwa.(Star), external

Kocin Tottenham Thomas Frank ya ce Kane, wanda ya fi kowa zura kwallaye a kulob din, ‘za su karbe shi da hannu biyu” idan ya dawo , amma ba ya tsammanin dan wasan zai bar kungiyarsa ta Jamus a yanzu.(Sky Sports), external

Dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, ya soma shirin barin Manchester United a watan Janairu domin neman wata kungiyar kwallon kafa .Ya samu wata kungiya da ta nemi a ba ta shi aro sai dai Man U ta yi watsi da tayin a bazara . (Mirror), external

Bayern Munich na tunanin sabunta kwantiragin dan wasan Faransa Michael Olise, mai shekara 23, bayan an alakanta shi da komawa Liverpool.(Liverpool Echo), external

Arsenal ta tuntubi dan wasan Turkiyya Kenan Yildiz, mai shekara 20, amma Juventus, wacce ta ki amincewa da tayin da Chelsea ta yi masa a lokacin bazara, ta kimanta shi kan Yuro miliyan 80 zuwa 100 . (Tutto Juve via Goal, external)

Chelsea na sha’awar dan wasan bayan Faransa Ismael Doukoure, mai shekara 22, wanda a halin yanzu yana kungiyar Strasbourg mallakar BlueCo, a dai dai lokacin da wasu kungiyoyin firimiya da dama ke zawarcinsa.(TBR Football), external

Aston Villa na son dan wasan gaban Ingila Jadon Sancho mai shekara 25 ya cigaba da taka mata leda na din din, Man U ce ta bada aron dan wasan ga Aston Villa. (National World)

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara