Connect with us

Fasaha

Kusan Malaman Makaranta Dubu 2 Ke Samun Horo a Barno

Published

on

 

Gwamnatin jihar Borno ta fara aikin horas da malamai 1,949 a matakin farko da aka gano cewa suna iya koyawa sakamakon gwajin cancantar da gwamnatin jihar ta gudanar.

 

Sakamakon jarabawar ya nuna cewa daga cikin malamai 15,823 da suka zana jarabawar, 5,257 ne kawai suka samu nasara; 6,227 sukayi kasa da abin da ake buƙata, amma an yi la’akari da cewa idan suka horarwa zasu iya ci gaba da aikin; yayin da 4,339 aka gano ba su da horo kana ba zasu iya aikin ba.

 

Da yake kaddamar da shirin a kwalejin ilimi ta Waka Biu da ke karamar hukumar Biu, gwamna Babagana Zulum ya ce shirin zai ci gaba da daukar nauyin mutane 2,730 da suka amfana.

 

“Hakika, a ranar 19 ga Maris, 2024, gwamnati ta amince da ware Naira biliyan daya (N1 biliyan) don horar da malamai 2,730. Wadannan malaman za su yi horo ne a kwalejin ilimi ta Waka-Biu da kwalejin kimiyya da fasaha ta Umar Ibn Ibrahim Elkanemi Bama, domin gudanar da shirin na tsawon watanni uku ga masu cin gajiyar 1,884,” in ji Zulum.

 

A cewar Gwamnan, kimanin malamai 846 da ba su da takardar shedar kammala jami’a za su yi shirin kammala karatun samun shaidar horasda malamai ta NCE.

 

Ya ce horon ya fara ne da nufin inganta harkar ilimi a jihar, inda ya ce kowane mahaluki zai samu horon kyauta tare da biyan naira 30,000 duk wata a kan albashin da ya saba karba.

 

Shugaban kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) reshen jihar Borno, Kwamared Zali Garba ya yabawa gwamna Zulum kan kawo sauyi a fannin ilimi.

 

Taron ya samu halartar Sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Mohammed Ali Ndume; Mai Martaba Sarkin Biu, Mustapha Umar Aliyu II; ‘yan majalisar dokokin jihar Borno; Kwamishinan ilimi, kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Lawan Abba Wakilbe da sauran manyan jami’an gwamnati.

 

Cov/Dauda/Wababe

Labarai

Labarai16 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai18 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai7 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara