Ilimi
Gwamnatin Jigawa Ta Bada Kwangilar Hanyar Kiyawa Zuwa Birnin Kudu
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta bayar da kwangilar aikin sake gina titin Kiyawa zuwa Birnin kudu.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar duba hanyar.
Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa da jinkirin da ake yi na gyaran hanyar da kuma sake gina magudanan ruwa a hanyar da aka bayar a bara.
Don haka Mallam Umar Namadi ya yi kira ga dan kwangilar da ke gudanar da aikin da ya gaggauta daukar mataki tare da kammala aikin kamar yadda aka tsara.
Gidan Rediyon Najeriya na Kaduna ya ruwaito cewa, Gwamnan ya kuma kai ziyarar gani da ido kan aikin titin Shuwarin, Wurma, Abaya da kuma Chamo zuwa Isari da ake yi.
Ya kuma ziyarci makarantar firamare ta Shuwarin Yamma da cibiyar kula da lafiya a matakin farko inda ya tattauna da malamai da ma’aikatan lafiya kan yadda za a tabbatar da ingancin aikin.
KARSHE/USMAN MZ/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
