Ilimi
Gwamnatin Jigawa Za Ta Samar Da Gidaje A Jami’ar Tarayya Da Ke Babura
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da tallafawa harkokin koyo da koyarwa a Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya dake karamar hukumar Babura.
Mataimakin Gwamnan jihar, Injiniya Aminu Usman ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin sabon shugaban gudanarwar jami’ar Oba Ajigbade Gbadegesin Ogunoye Olowo na Owo na uku a ofishinsa dake Dutse babban birnin jihar.

Mataimakin Gwamnan wanda ya sami wakilcin Shugaban Ma’aikata na jihar Alhaji Muhammed Dagacheri, yace Gwamna Umar Namadi ya bada umarnin gina gidaje da kuma samar da kayayyakin koyo da koyarwa domin baiwa malaman jami’ar kwarin gwiwar gudanar da ayyukan su.
Kazalika, ya bada tabbacin gwamnatin jihar na ci gaba da tallafawa jami’ar domin amfanin ‘yan jiha da ma kasa baki daya.

A jawabin sa, sabon shugaban gudanarwar jami’ar, basarake Oba Ajigbade ya yabawa gwamnatin jihar Jigawan bisa tallafawa jami’ar a koda yaushe.
A don haka, ya bada tabbacin ciyar da Jami’ar gaba a matsayinsa na shugaban gudanarwarta na farko, tare da neman hadin kan gwamnatin da ma al’ummar jihar domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Tun farko a jawabin sa, shugaban jami’ar Farfesa Sabo Birnin Kudu yace sun zo ofishin mataimakin Gwamnan ne domin gabatar da sabon shugaban gudanarwar jami’ar da kuma godewa gwamnatin jihar bisa tallafin da take bai wa jami’ar.
Yana mai cewar jami’ar ta na da yawan dalibai dubu daya da ma’aikata 180 da kuma Kwasa-kwasai guda goma sha takwas da take gudanarwa.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
